in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an gwamnatin Sin sun bayyana halin da Sin ke ciki wajen yin gyare-gyare game da tsarin al'adu na kasar
2012-11-12 11:21:51 cri

Jiya Lahadi 11 ga wata, aka yi taron manema labaru karo na 3 a cibiyar yada labaru na babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Jami'an gwamnatin Sin guda 4 da suka fito daga sashen kula da harkokin fadakar da jama'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da ma'aikatar al'adu, da hukumar kula da harkokin gidajen telebijin da radio, kana da hukumar kula da harkokin dab'i ta Sin sun yi bayani ga 'yan jaridu na gida da waje sama da 300 game da tsarin yin gyare-gyare ta fuskar al'adu na kasar Sin da kafa tsarin al'adu domin jama'a.

A gun taron, mataimakin sashen kula da harkokin fadakar da jama'a na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma darektan ofishin kula da harkokin yin gyare-gyare game da tsarin al'adu da raya harkokin al'adu na kwamitin tsakiya na kasar Sin Sun Zhijun ya bayyana cewa, bayan da aka yi babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 16, an bude wani sabon shafi wajen raya al'adu na kasar Sin, kuma an samu wata sabuwar hanyar raya al'adun gurguzu da ke da halayyen musamaman na kasar Sin. Bisa tunanin taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, za a kara raya harkokin al'adu na kasar Sin, don gina kasar Sin mai wadatar al'adu iri na gurguzu.

Mataimakiyar ministan al'adu ta kasar Sin Zhao Shaohua ta bayyana cewa, bayan da aka yi babban taron jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 16, an karfafa aikin yin gyare-gyare game da tsarin al'adu na kasar Sin, kuma an kara sa ido kan kasuwannin al'adu na kasar, hakazalika an kara gina abubuwan more rayuwa da suka shafi harkokin al'adu tare da kafa tashar al'adu a garuruwa da gundumomi na kasar Sin, kana an ci gaba da gudanar da ayyukan da suka shafi labaru game da al'adu da sauransu.

Haka kuma, an kara sa himma wajen aikin kare kayayyakin al'adu da aka gada daga kaka da kakani.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China