in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar da kasar Sin take bi wadda kowa ke nuna yabonsa
2012-11-11 17:00:24 cri
A lokacin da ake gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kasashen duniya sun nuna yabo ga hanyar da kasar Sin take bi wajen samun ci gaba a shekaru 10 da suka wuce, suna ganin cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ta sami babban ci gaba kamar hakan, shi ne tsayawa tsayin daka da ta yi kan bin hanyar gurguzu mai alamar kasar Sin.

Shugaban cibiyar nazari kan albarkatun kudancin Afirka ta kasar Afirka ta Kudu, Kabenba wanda ya bayyana hakan yace kasar Sin ta samar da wata hanyar da kowa ke nuna mata yabo.Inda ta kara karfinta yayin da jama'ar kasar suka kara samun kudin shiga a sakamakon haka. A sa'i daya kuma, hanyar ta zama abin koyi ga dukkan kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka.

Mataimakin shugaban jam'iyyar Freedom ta Australia, Bishop ya bayyana cewa, tsayawa tsayin daka kan hanyar samun bunkasuwa cikin lumana da kasar Sin take yi, ta fidda mutane sama da miliyan 100 daga talauci. Ba a taba samun irin wannan sakamako mai kyau a tarihin bil'adam ba.

Ra'ayinsa ya dace da wani bayanin da aka gabatar a jaridar Kasuwanci ta Jamus, inda aka yi sharhin cewa, kowa ya san babban ci gaban da kasar Sin ta samu tun bayan da aka fara gudanar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida. Kasar Sin ta kasance kasa ta farko, ko kuma kasa daya tak a duniya wajen fidda mutane sama da miliyan 100 daga talauci a karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis.

Haka kuma a nasa bangare wani dalibi mai karatun digiri na uku a jami'ar Paris ta takwas ta Faransa, Pierre Pical yana ganin cewa, Sin za ta kawo wa duniya wata sabon salo wajen samun ci gaba, wadda ta fi na yanzu a fannin zaman lafiya da jituwa.

In ji shi hanyar da ake bi, muhimmin batu ne ga kowace kasa. Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta samu wata hanyar da ya dace da yanayi da kuma al'adar kasar Sin. Jama'ar kasar da ta sauran kasashen duniya sun riga sun ci gajiyarta.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China