in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin shugabanni na babban taron wakilan JKS karo na 18 ya shirya taro na 2
2012-11-10 19:32:51 cri
Ranar Asabar 10 ga wata da yamma, a nan Beijing, rukunin shugabanni na babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 ya shirya taro na 2, inda Hu Jintao ya shugabanta.

Xi Jinping, babban sakatare mai kula da harkokin babban taron jam'iyyar ya yi karin bayani kan sunayen mutanen da aka shirya zaba a matsayin 'yan takarar neman zama mambobin kwamitin tsakiya karo na 18, da mambobin da aka kara, da mambobin babban kwamitin ladabtarwa karo na 18.

Har wa yau a yayin taron, an amince da mika wa wakilan jam'iyyar daftarin kudurin rahotannin da kwamitin tsakiya karo na 17, da babban kwamitin ladabtarwa karo na 17 suka gabatar, da ka'idojin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka gyara don su yi tattaunawa a kansu.

Sa'an nan an amince da mika wa wakilan jam'iyyar sunayen da aka ambata a baya don su yi nazari.

Haka zalika a yayin taron, an amince da hanyar da za a bi wajen yin zabe a yayin babban taron wakilan jam'iyyar karo na 18, wadda wakilan jam'iyyar suka yi nazari a kanta. Kana kuma, an amince da sunayen masu sa ido kan jefa kuri'a, wadanda za a gabatar da su ga babban taron a lokacin jefa kuri'a a hukumance. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China