in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS za ta kara kyautata tsare-tsarenta da za su raya jam'iyyar ta hanyar kimiyya
2012-11-10 17:30:22 cri






Yanzu haka ana gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a nan birnin Beijing. A cikin rahoton da ya gabatar wa wakilan jam'iyyar don su yi nazari, Hu Jintao, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yi karin bayani kan yadda za a kara kyautata jam'iyyar, inda kuma sau da dama ya ambaci kafa tsare-tsaren jam'iyyar.

Kwanan baya, Wang Jingqing, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin 'yan jam'iyyar na kwamitin tsakiya na JKS ya bayyana cewa, JKS za ta kara kyautata tsare-tsarenta, a kokarin raya kanta ta hanyar kimiyya. To, abokiyar aikinmu Tasallah ta hada mana rahoto!

Yanzu akwai 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin fiye da miliyan 80, lamarin da ya sanya JKS ta kasance tamkar jam'iyya mafi yawan mambobi a duniya, wadda take mulkin kasa. Wadannan 'yan jam'iyyar suna kuma kasancewa tamkar ginshikai wajen raya kasar Sin. Ba tare da boye kome ba mista Wang Jingqing ya bayyana mana cewa, JKS na fuskantar kalubaloli daban daban, inda ya ce, "A cikin sabon halin da ake ciki, jam'iyyarmu na bukatar kara raya kanta ta hanyar kimiyya a fannoni daban daban, kamar su mulkin kasa, yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, gudanar da harkokin tattalin arziki bisa bukatun kasuwanni, yanayin da ake ciki a kasashen ketare, lamarin da ya karfafa gwiwarmu wajen ci gaba da kyautata kwarewar mulkin kasa da ba da jagoranci."

A cikin rahoton da mista Hu Jintao ya gabatar a yayin bikin bude taron, ya ambaci cewa, wajibi ne a ci gaba da yin gyare-gyare kan tsarin nada jami'ai da kuma wadanda suka yi fice wajen mulkin kasa. Wang Jingqing ya nuna cewa, JKS za ta ci gaba da nada jami'anta bisa kwarewarsu, a kokarin kafa wani tsarin nada jami'ai mai dacewa kuma maras sauye-sauye. Mista Wang ya ce, "Ya zuwa shekarar 2020, za mu kafa tsare-tsare guda 4 a fannin nada jami'ai, kamar zaba da nada wanda ya fi dacewa, jarraba jami'ai, sa ido kan jami'ai da kuma karfafa gwiwar jami'ai wajen gudanar da ayyukansu."

Haka zalika Wang Jingqing ya sha jaddada cewa, tsayawa tsayin daka kan mayar da mutane a gaba da kome, gudanar da harkokin kasa domin biyan bukatun jama'a, da kafa huldar kud-da-kud tare da al'umma su ne abubuwan da JKS ta sanya gaba ta fuskar siyasa. Mista Wang ya ce,"Har kullum ya zama tilas a mayar da batun kiyaye moriyar jama'a a gaba da kome, muna gudanar da ayyukanmu ne domin ganin jama'a sun samu babbar moriya, mun kuma kiyaye babbar moriyarsu yadda ya kamata."

Har wa yau kuma, a game da shakkar da ake yi wa JKS dangane da kafa sassanta a masana'antu masu zaman kansu, Wang Jingqing ya amsa cewa, kafa sassan JKS a masana'antu masu zaman kansu ya dace da dokokin kasar da ka'idojin JKS, haka kuma yana iya kara hada kan ma'aikata, kara fahimtar bukatunsu, taimakawa masana'antun su kara sanin manufofin kasar Sin cikin sauri, warware sabanin da ke tsakanin ma'aikata, a kokarin kafa kyakkyawar dangantaka a cikin wadannan masana'antu masu zaman kansu, lamarin da ya samu marhabin da goyon baya daga masana'antun. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China