Johnson Aseidu Nketia, babban darektan jam'iyyar NDC ta kasar Ghana ya bayyana cikin wasikarsa ta fatan alheri cewa, JKS ta dace da yanayin da ake ciki ta fuskar siyasa, tattalin arziki, al'adu da dai sauransu. Jam'iyyarsa na son ci gaba da raya huldar kud-da-kud da JKS, tare da inganta zumunci da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 da jama'arsu duka.
Ban da wannan kuma, a cikin wasikarsa ta fatan alheri, Omer Hassan Ahmed El Bashir, shugaban jam'iyyar babban taron kasar Sudan kuma shugaban kasar ya ce, babban taron wakilan JKS karo na 18 na da matukar muhimmanci, wanda zai himmantu wajen tabbatar da ganin jama'ar Sin sun ji dadin zaman rayuwarsu, ana raya kasa ta hanyar kimiyya, al'ummomin kabilu daban daban na kasar sun hada kansu domin aiwatar da fasahohin raya kasa, har wa yau kuma, a yayin da ake gudanar da taron, ana samun muhimman sauye-sauye a kasa da kasa, inda kasar Sin da ma jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin suke taka muhimmiyar rawa mai yakini. (Tasallah)