Yau ranar 9 ga wata da safe, a yayin da yake tattaunawa da wakilan da suka fito daga lardin Jiangsu, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya nuna cewa, rahoton da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta gabatar a yayin bikin bude taron ya kasance tamkar wata sanarwa da kuma matakan da aka tsara dangane da yadda za a samu sabuwar nasara a fannin raya gurguzu mai halin musamman na kasar Sin a cikin sabon halin da ake ciki. Don haka, wajibi ne a fara yin koyi da kuma aiwatar da tanade-tanaden da ke cikin wannan rahoto, kuma a fahimci nauyi da ayyukan da aka danka, a ci gaba da yin hadin gwiwa da gwagwarmaya, a kokarin kara samun nasara cikin babban sha'anin raya gurguzu mai halin musamman na kasar Sin. (Tasallah)