in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya na mai da hankali sosai kan babban taron wakilan JKS
2012-11-09 17:15:10 cri






Tun lokacin da Sin ta aiwatar da tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, musamman ma a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kasar ta samu ci gaban a zo a gani a fannoni daban-daban ciki har da siyasa, tattalin arziki, kimiyya, al'umma, aikin soja da sauransu, kuma ta zama wani babban ginshiki a duniya. Babban taro karo na 18 na jam'iyyar kwaminis ta Sin (JKS) da ake yi yanzu haka, zai tsai da sabbin tsare-tsare ga bunkasuwar kasar Sin nan gaba, a yayin da bunkasuwar kasar Sin ke kawo tasiri sosai ga bunkasuwar kasashen duniya. Haka ya sa kasashen ke dora muhimmanci sosai kan taron.

Kasashe daban-daban na duniya na mai da hankali sosai kan wannan babban taron da kasar Sin take yi. Kamar yadda Amurka ta kammala zaben shugabanta ba da dadewa ba, ita ma Sin a cikin taron da take yi, zata canja shugabannin ta. Yadda sabbin shugabannin kasashen biyu za su kula da dangantakar dake tsakanin su ya zama muhimmin aiki dake jawo hankali kafofin yada labaru da 'yan siyasa na kasar Amurka. Tsohon jakadan kasar Amurka dake kasar Sin Staples Roy ya ce:

"Muhimmin aikin da aka sa gaba game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu shi ne, wadannan kasashe biyu a matsayin kasashe masu girma a duniya, ya kamata, su daidaita dangantakar dake tsakaninsu na kasa mai kasa mai wadata da na tasowa. Wannan ba abu mai sauki ba a tarihi cikin tarihi ba, har ma a kan samu rikici. Shugabannin kasashen biyu sun fahimci wannan batu, tare kuma sun da tsai da tsari domin kaucewa duk wani sabani da za a iya fuskanta. Sai dai har ila yau, ba mu shigo da dukkan ayyuka ko matakan da muke dauka cikin wani buri na kafa dangantakar hadin kai cikin daidaito ba. Ya kamata, sabbin shugabannin kasar Sin su mai da muhimmanci kan wannan batu, kuma Barack Obama wanda ya cimma nasarar ci gaban da mulkinsa, ya kamata ya yi kokari daidaita wannan batu. Hakan ya sa, taron da Sin take yi ke da muhimmanci sosai, saboda zai fito da sabbin shugabannin kasar."

Game da wannan babban taro, kafofin yada labaru na kasa da kasa su ma suna mai da hankali sosai. Shugaban reshen kamfanin dillancin labarai ta kasar Rasha ITAR-TASS dake birnin Beijing, Andrey Killirov ya saurari rahoton da aka gabatar a wajen taron a ran 8 ga wata, kuma ya ce:

"Rahoton ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da taka rawa cikin harkokin kasa da kasa da ya shafi bangarori daban-daban, da kuma goyi bayan wasu kungiyoyin kasa da kasa ciki har da kungiyar hadin kai ta birnin Shanghai (SCO), kungiyar BRICS. Abin da yake da muhimmanci gaske ga kasar Rasha. Saboda Sin da Rasha na hulda sosai da juna cikin wadannan kungiyoyi, kamar su MDD, SCO da BRICS, ban da haka, suna daukar matsaya daya ko kusan daya kan wasu manyan batutuwan kasa da kasa."

Ban da 'yan siyasa da manema labaru, taron yana kuma jawo hankali masu nazari na kasa da kasa.

Wani shehun malami a jami'ar Nairobi na kasar Kenya mai koyar da ilmin siyasa, Kimani Njogu ya ce, ganin yadda za a canja shugabannin kasar Sin cikin taron da ake yi, kuma kasar Kenya ma za ta yi zaben shugaban kasar a shekara mai zuwa, ko shakka babu, sabbin shugabannin kasashen biyu za su ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. Kuma bunkasuwar kasar Sin na taimaka sosai ga kasashen Afrika. Kimani Njogu ya ce:

"Idan ana son samun bunkasuwar wata kasa, da farko ya kamata a tabbatar da manyan kayayyakin more rayuwa. A cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta taimakwa kasar Kenya wajen gina manyan kayayyakin more rayuwa. Ko shakka babu, manyan kayayyakin more rayuwa da Sin ta ba da taimako wajen gina su, sun yi amfani sosai ga jama'ar kasashen Afrika ciki har da jama'ar kasar Kenya. A ganina, mafitar nahiyar Afirka ba ta danganta ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen yamma ba, a maimakon haka danganta ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Asiya ciki har da kasar Sin."

Shugaban ofishin nazarin tsare-tsare ta kasar Faransa kuma manjo janar na rundunar sojan kasa na kasar Faransa Eric de La Maisonneuve, wanda gwani ne mai bincike batutuwan kasar Sin, ya ce, taron zai nuna hanyar siyasa da Sin za ta bi nan gaba, kuma ba da tasiri ga tattalin arzikin kasar. Haka kuma taron zai kara karfin kasar Sin a idon duniya. Ya ce:

"Yanzu, duniya na fuskantar wasu matsaloli, bai kamata ba, kasashe da dama na bayyana mawuyacin halin da suke ciki, ya kamata, wasu yankuna su tabbatar da zaman karkonsu ciki har da kasar Sin. Ci gaban da Sin ta damu wajen bunkasa tattalin arziki cikin gida na kawo amfani sosai ga kasa da kasa, saboda Sin na ba da taimakonta yadda ya kamata ga duniya. Idan Sin ta samu bunkasuwa mai kyau, duniya za ta samu farfadowa. Wannan ya kasance dalilin da ya sa muka dora muhimmanci sosai kan taron. Kuma muna sa ran alheri ga taswirar bunkasa tattalin arziki da siyasa da taron zai fitar za ta kawo amfani sosai ga tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar duniya.". (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China