in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsakaicin yawan kudin shiga da gwamnatin Sin ta samu ya karu da kashi 20.82 cikin 100 cikin shekaru 10 da suka gabata
2012-11-09 17:07:06 cri
Bisa bayanin da ministan harkokin kudi na Sin Xie Xuren ya rubuta a shafin ma'aikatar kudi ta kasar Sin, an ce, yawan kudin shiga da gwamnatin Sin ta samu ya karu daga kudin Sin RMB biliyan 1890 a shekarar 2002, zuwa kudin Sin RMB biliyan 10370, al'amarin da ke nuna habaka da kashi 0.82 cikin 100.

A cikin bayanin, an takaita nasarorin da sha'anin kudi na Sin ya samu bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 16 na kwamitin tsakiya, kuma a cikin bayanin, an ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, karkashin tsarin raya tattalin arziki dake kyautata kuma cikin hanzari, Sin ta ci gaba da yin gyare-gyare game da harkokin kudi, kuma ta kafa tsarin karuwar kudin shiga na kasar, matakin da ya sa yawan kudin shiga da Sin ta samu ya dinga karuwa, a sa'i daya kuma, bisa bukatun sauyin kasuwanni, da ci gaba a aikin gwamnati, Sin ta kyautata sha'anin kudin kasar, ta kuma kara yawan kudin da ake kebewa wajen ilmi, kiwon lafiya, abubuwan more rayuwa, da samar da guraben aikin yi.

Abin da ya fi muhimmanci shi ne, gwamnatin tsakiya ta kebe kudin da yawansu ya kai kudin Sin RMB biliyan 6000 wajen aikin gona, manoma da, kauyuka, haka zalika yawan karuwar kudin da aka samu ya zarce kashi 20 cikin 100, kuma gwamnatin Sin ta kara kaimi wajen aikin gona, wanda zai yalwata kauyuka, a kuma ayyukan gyare-gyare a yankunan.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China