in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun halarci tattaunawar da tawagogin jam'iyyar kwaminis suka yi
2012-11-09 10:31:04 cri

Jiya Alhamis 8 ga wata, aka bude taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a babban dakin taron jama'a, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gabatar da rahoton da ke da lakabi "Dagewa kan hanyar gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar Sin, don cimma nasarar zaman wadata a dukkan fannoni". A kuma wannan rana ne da yamma, shugabannin kasar Sin Wu Bangguo, Wen Jiabao, Jia Qinglin, Li Changchun, Xi Jinping, Li Keqiang da dai sauransu suka halarci zaman tattaunawa tare da tawagogin jam'iyyar kwaminis da suka zo daga sassa daban daban na kasar.


Yayin tattaunawar, sun bayyana cewa, muhimmin batun cikin jawabin da Mr. Hu ya gabatar shi ne tsayawa kan matsayin Markisanci, rahoton ya zamanto babbar ka'idar siyasa da kasar Sin mai bin tsarin gurguzu za ta bi don samun nasara a karkashin sabon yanayin da ake ciki, ganin ita ce hanyar da za a bi don samun wadata a dukkan fannoni. Kamata ya yi a tsaya kan tsarin gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar Sin, da kara kokari a fuskar karfafa tsarin yin shawarwari ta demokuradiyya da ke da irin halaye na gurguzu, gami da aiwatar da dukkan matakan da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis karo na 18 ya tsara, da ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa, don a tabbatar da samun wadata daga dukkan fannoni.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China