in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabanni, jam'iyyu da kungiyoyi na kasa da kasa sun taya JKS murnar bude babban taron wakilai karo na 18
2012-11-08 20:52:16 cri
A yayin da ake gudanar da babban taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a nan birnin Beijing, wasu shugabanni, jam'iyyu da kungiyoyi na kasa da kasa sun aiko da wasiku ko sakon tangarahu domin taya JKS murnar bude babban taron wakilanta.

A sakonsa na tangarahu a madadin jam'iyyarsa, Hama Amadou, shugaban jam'iyyar neman kawance da shimfida dimokuradiyya Afirka ta kasar Nijar kuma shugaban majalisar dokokin kasar ya nuna fatansa na ganin an kammala babban taron wakilan JKS a wannan karo cikin cikakkiyar nasara, ya kuma yi wa kasar Sin murnar samun nasarori a karkashin shugabancin JKS. Sa'an nan kuma, Hama Amadou ya ce, a shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta samu manyan nasarori wajen samun wadata da bude kofa ga kasashen duniya, lamarin da ya samu babban yabo daga kasa da kasa. Haka kuma, Hama Amadou ya yaba wa bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasashen Afirka da Sin kwarai da gaske.

A wasikar da ta aiko, jam'iyyar ANC ta kasar Afirka ta Kudu ta ce, a yayin da JKS take gudanar da babban taron wakilanta karo na 18, shugabannin jam'iyyar ANC da 'yan jam'iyyar da ma jama'ar Afirka ta Kudu baki daya sun nuna fatan alheri kan gudanar da babban taron wakilan JKS a wannan karo cikin nasara. Har wa yau kuma, Blade Nzimande, babban darektan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Afirka ta Kudu ya bayyana a cikin wasikarsa ta fatan alheri cewa, Jam'iyyar Kwaminis ta Afirka ta Kudu ta yi imanin cewa, JKS za ta tsai da muhimmin kuduri a yayin babban taron a wannan karo, inda kuma za ta zabi sabbin shugabanni, da fito da shirin raya jam'iyyar, lamarin da zai raya JKS zuwa sabon mataki. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China