in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta) An bude babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18
2012-11-08 16:07:04 cri

Yau Alhamis 8 ga wata da safe, a nan birnin Beijing, an bude babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin mai mulki, karo na 18 a hukunce, a madadin kwamitin tsakiya karo na 17, babban sakatare na kwamintin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Hu Jintao, ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta shugabanci kasar Sin don ci gaba da bin hanyar gurguza mai tsari na musamman da ya dace da kasar Sin.

A cikin rahoton da Mr. Hu ya gabatar wa dukkan wakilan jam'iyyar, ya jaddada cewa, hanyar gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar Sin, da tsarin ilmi na gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar Sin, sun kasance nasarorin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jama'ar kasar suka samu cikin shekaru sama da 90 da suka gabata, dole ne mu ci gaba da binsu, da kokarin raya su, haka kuma ra'ayin raya kasa bisa kimiyya, ya zama wani sabon kashi na tsarin gurguzu da ke da halayyen musamman da kasar Sin ta samu da dole ne jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta tsaya haikan a kai.

An kaddamar da wannan taron a yayin da kasar Sin ta shiga wani muhimmin lokaci na kokarin samun zaman wadata daga dukkan fannoni, kuma a cikin rahoton da Mr. Hu ya gabatar, ya bayyana bukatun da ake da su a fagen samun zaman wadata daga dukkan fannoni, kuma a cewarsa, babban burin da aka saka a gaba shi ne, ya zuwa shekara ta 2020, a ninka yawan kudin samar da kayayyaki na GDP, da albashin na mazaunan birane da kauyuka sau biyu bisa na shekarar 2010, tare da kara samun ingancin bunkasuwa.

Haka kuma, a cikin rahoton, an tsara shirye-shirye game da raya harkokin tattalin arziki, siyasa, tsaro, da diplomasiyya da dunkulewar kasa, da raya jam'iyyar kwaminis ta kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China