in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS ta bayyana wa duniya kan yadda take tsaya tsayin da kuma hanyar da take bi
2012-11-08 15:02:23 cri






Yau ranar 8 ga wata, an kaddamar da wani mako na "tsai da makomar kasar Sin a nan gaba" a bakin kasashen duniya a nan birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar, wato an bude babban taro karo na 18 na wakilan JKS, wadda ta kasance jam'iyyar da ke mulkin kasar Sin. A yayin bikin bude taron, Hu Jintao, babban daraktan JKS, kuma shugaban kasa mai barin gado ya ba da wani muhimmin rahoto. Sakamakon tabbatar da JKS a matsayin jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar a cikin tsarin mulkin kasar, wani muhimmin kashi cikin wannan rahoto shi ne, tsara manufofi da matakan da JKS za ta aiwatar a cikin shekaru 5 masu zuwa ko fiye domin jagorantar kasar Sin zuwa ga ci gaba.

Ganin yadda JKS ke tinkarar da kalubaloli da yawa yayin da take mulkin kasar, sannan kuma yadda kasar Sin za ta zabi hanyar bunkasuwa a nan gaba ta jawo hankalin kasashen duniya sosai, shi ya sa Hu Jintao ya furta a farkon rahoton don sheda ra'ayin jam'iyyar kan batun. Yana mai cewa,

"babban taken taron shi ne, a daga tutar bin tsarin gurguzu na salon musamman na kasar Sin a karkashin jagorancin hasashen marigayi Deng Xiaoping, hasashen wakiltar karfin ci gaba na zamani da al'adun zamani kana da babbar moriyar jama'a, da kuma hasashen samun ci gaba bisa ilmin kimiyya. Kuma a samu 'yancin nazari, bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, hada gwiwa, tsallake wahalhalu, tare da tsayawa tsayin daka kan bin hanyar gurguzu mai tsarin musamman ta kasar Sin ba tare da canzawa ba, a kokarin raya al'umma mai wadata."

"Tsayawa tsayin daka" wannan jimla ta sheda nacewar da JKS ta yi a kan hanyar gurguzu mai tsarin musamman ta kasar Sin, abin da ya bai wa kasashen waje amsa kan yadda JKS za ta zabi hanyar ci gaba a nan gaba.

A cikin wannan rahoto kuma, Hu Jintao ya yi bayani filla filla kan ayyukan JKS na nan gaba domin warware matsalolin da kasar Sin ke fuskanta a yanzu yayin da take raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta.

Rahoton ya nuna cewa, kasar Sin za ta yi kwaskwarima ga tsarin tattalin arzikinta daga dukkan fannoni, da aiwatar da manufar kara azama ga kirkire-kirkire don cigaba, da sa kaimi ga bunkasuwar birane da karkara bai daya, kana da kyautata aikin bude kofa ta fuskar tattalin arziki.

Ban da wannan kuma, rahoton ya nanata muhimmiyar ma'anar yin gyare-gyare ga tsarin siyasa, inda aka gabatar da matakan a zo a gani wajen goyon baya da tabbatar da ganin yadda jama'a za su tafiyar da hakkinsu a cikin babban taron wakilan jama'ar kasar Sin, a ciki an ambaci batun kara yawan wakilan jama'a daga kananan hukumomi. Hu ya furta cewa,

"Za a kara yawan wakilan jama'a daga kananan hukumomi, kamarsu ma'aikata, manoma, da kuma masu ilmi, yayin da rage yawan wakilan jama'a da suka kasance kamar kusoshin jam'iyyar da na gwamnati. Haka kuma za a kafa hukumar tuntubar wakilai a majalisar domin kyautata tsarin tuntuba a tsakanin wakilai da jama'a."

Ba da tabbaci da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a domin su more nasarorin da kasar Sin ta samu wajen bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, shi ma wani muhimmin aiki na JKS a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata. Rahoton babban taro karo na 18 na wakilan JKS da shugaba mai barin gado Hu Jintao ya gabatar ya sake tabbatar da muhimmancin wannan aiki, inda aka yi alkawarin gudanar da ayyukan koyarwa da za su gamsu da jama'a, kyautata ingancin sha'anin samar da guraban aikin yi, kara yawan kudin shiga na jama'a, sa kaimi ga ci gaban tsarin ba da tabbaci ga zaman al'umma na birane da karkara, kyautata lafiyar jikin jama'a, kana da dora muhimmanci kan aikin gudanarwa da ya shafi zaman al'umma. Hu Jintao ya jaddada cewa, jama'a ba za su iya more sakamakon ci gaba da aka samu ba, sai dai in an kara yin kwaskwarima ga tsarin rarraba kudin shiga.

Sakamakon saurin ci gaban tattalin arziki, kasar Sin tana tinkarar matsin lamba a fannonin makamashi da muhallin halittu. Game da batun, rahoton ya bayyana cewa, kiyaye muhallin halittu na da nasaba da alherin jama'a da kuma makomar al'umma, kana zai ba da taimako wajen tsaron muhallin halittu a duk duniya. Yadda za a yi amfani da filaye yadda ya kamata zai zama wani muhimmin batu wajen kiyaye muhallin halittu. Hu ya ce,

"Za a kayyade amfani da filaye fiye da kima, da daidaita tsarin amfani da su bisa ka'idar cimma daidaito a tsakanin mutane da makamashi da kuma muhallin halittu, kana da cimma daidaito a tsakanin muradun tattalin arziki da na al'umma da kuma na halittu tare, domin bai wa zuriyoyinmu wani gida mai kayatarwa da za a iya ganin sararin sama mai launin shudi, filaye masu launin kore, da kuma ruwa mai tsabta."

Bugu da kari kuma, rahoton ya nanata cewa, yaki da cin hanci da rashawa ra'ayi ne da JKS ke dauka a ko da yaushe. Rahoton ya ce, za a ci gaba da tafiyar da ka'idojin da suka shafi amfani da iko yadda ya kamata, tare kuma da sanya ido kan yadda muhimman kusoshin jam'iyya ke amfani da ikonsu.

Rahoton ya kuma nuna cewa, kasar Sin za ta bi ka'idojin zaman lafiya da bunkasa da hadin gwiwa don moriyar juna yayin da take daidaita dangantaka a tsakaninta da kasashen waje. Hu Jintao ya bayyana cewa,

"Za mu kyautata da kuma raya dangantaka tare da kasashe masu ci gaba, inganta hadin kansu, daidaita sabane-sabane a tsakaninmu yadda ya kamata, domin neman kafa kyakkyawar dangantaka ta sabon salo a tsakanin manyan kasashe cikin dogon lokaci."

Jama'ar kasar Sin na son zaman lafiya da ci gaba, za su kokarta tare da jama'a na kasa da kasa domin neman samun zaman lafiya da ci gaban bil Adam tare, a cewar rahoton.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China