in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar da Sin ta samu ta yi amfani ga kasashen Afrika
2012-11-08 11:10:44 cri
A yanzu haka Sin na gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar JKS ta kasar, a yayin wannan muhimmin lokaci, wani shehun malami a jami'ar Nairobi na kasar Kenya mai koyar da ilmin siyasa, Kimani Njogu ya nuna fatan alheri ga babban taron, kuma ya jaddada cewa, ci gaban da Sin ta samu yana da amfani sosai ga kasashen Afrika.

Yayin da Kimani Njogu ya ke hira da wakilinmu, ya ce, Sin ba ta kawo ko wane barazana ba, a maimakon haka, kasashen Afrika na samun fa'ida daga kasar Sin. Ya ce, idan ana son samun bunkasuwar wata kasa, da farko ya kamata a tabbatar da manyan kayayyakin more rayuwa. A cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta taimakwa kasar Kenya wajen gina manyan kayayyakin more rayuwa. Ko shakka babu, manyan kayayyakin more rayuwa da Sin ta ba da taimako wajen gina su, sun yi amfani sosai ga jama'ar kasashen Afrika ciki har da jama'ar kasar Kenya. A ganinsa, mafitar nahiyar Afirka ba ta danganta ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen yamma ba, amma ta danganta ga raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Asiya ciki har da kasar Sin.

Ban da haka, Kimani Njogu ya ce, babban taron da Sin ke yi zai canja shugabanninta, kuma Kenya ma za ta gudanar da babban zabe a shekara mai zuwa, ba shakka sabbin shugabannin kasashen biyu za su kara azama ga dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China