A madadin kwamitin tsakiya karo na 17, babban sakatare kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Hu Jintao ya gabatar da rahoto, kuma wakilan jam'iyyar za su duba rahoton nasa. A cikin wannan rahoto, an ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta shugabanci kasar don tabbatar da ci gaba da bin hanyar gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar Sin.
Babban taron wakilan jam'iyya da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya zama hukumar koli ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma a kan yin taro a ko wadanne shekaru biyar-biyar. Yanzu, akwai mambobin 'yan jam'iyyar kwaminis da yawansu ya kai sama da miliyan 80, kuma wakilan mambobin 'yan jam'iyyar da yawansu ya kai sama da 2200 da aka zabe su sun halarci taron, kuma , wakilan mambobin 'yan jam'iyya da suka shiga jam'iyyar bayan da aka gudanar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978 sun yi rinjaye a cikinsu.
Bisa ajandar taron, a cikin kwanaki 7 masu zuwa, wakilai mahalartar taron za su duba rahoton da Mr. Hu ya gabatar, kuma za a zartas da gyararren tsare-tsare na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, sannan za a duba rahoton da kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar ya gabatar, gami da zaben sabon kwamitin tsakiya da sabon kwamitin ladabtarwa na kasar Sin.(Bako)