in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18
2012-11-07 21:55:56 cri






Za a bude babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a safiyar ranar 8 ga wata a nan birnin Beijing. A gun taron manema labaru da aka gudanar a ranar 7 ga wata, kakakin kula da harkokin watsa labaru na babban taron Cai Mingzhao ya yi bayani game da abubuwan da suka shafi babban taron a wannan karo. A taron manema labarun da aka shafe tsawon sa'o'i kimanin biyu, Cai Mingzhao ya amsa tambayoyi a fannonin kyautata zaman rayuwar jama'a, yaki da cin hanci, yin kwaskwarima kan tsarin siyasa da sauran batutuwan da jama'ar kasar Sin da 'yan jarida na gida da waje suka mai da hankali a kai sosai. Wannan ya bayyana cewa, akwai fahimtar juna a tsakanin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake kan karagar mulki da jama'ar kasar.

A gun taron manema labarun, Cai Mingzhao ya bayyana cewa, za a tsara manufofi kan yadda za a raya zamantakewar al'ummar kasar Sin a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar a wannan karo. Ya ce, "Babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 wani muhimmin taro ne yayin da ake bunkasa zamantakewar al'ummar kasar, ci gaba da aiwatar da manufar bude kofa da yin kwaskwarima, da kuma gaggauta gyara hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasar. A gun taron, za a yi nazarin abubuwan da suka wakana a shekaru biyar da suka wuce da kuma fasahohin da aka samu bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 16, tsara manufofin da suke dacewa da bukatun jama'ar kasar da halin da kasar ke ciki, da kuma tsara manyan tsare-tsare kan yadda za a ci gaba da aiwatar da manufar bude kofa da yin kwaskwarima tare da raya zamantakewar al'umma da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin."

Cai Mingzhao ya bayyana cewa, bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 16, jam'iyyar da gwamnatin kasar Sin sun yi kokari wajen kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar, kuma sun cimma wasu nasarori. Amma gibin dake tsakanin masu arziki da matalauta yana karuwa, lamarin da ya jawo hankali kasa da kasa.

Game da wannan batu, Cai Mingzhao ya ce, bisa manufofin dora muhimmanci kan zaman rayuwar jama'a da taimaka musu wajen samun wadata da aka tsara, za a shirya ayyukan tabbatar da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar Sin a gun babban taron a wannan karo. Ya ce, "Bisa halin bunkasuwa da kasar Sin take ciki da bukatun jama'ar kasar na samun rayuwa mai kyau, za a dora muhimmanci kan yadda za a tabbatar da kyautata zaman rayuwar jama'a, kyautata tsari a wannan fanni, kafa tsarin ba da hidima, yin kokarin samun ci gaba a fannonin ba da ilmi, samar da aikin yi, kiwon lafiya, gidajen kwana da dai sauransu, wannan zai mataki zai kara taimakawa jama'a."

A lokacin da take kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a, yadda za ta yi yaki da matsalolin cin hanci da rashawa, wannan ma fata ne da jama'a ke nuna wa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ta dade tana rike ragamar mulkin kasar Sin. A 'yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da dimbin matakan yaki da matsalolin cin hanci da rashawa. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ma ta yi kira da ya yi kokarin yaki da matsalolin cin hanci da rashawa.

A yayin taron manema labaru da aka yi yau da yamma, Mr. Cai Mingzhao ya bayyana cewa, a yayin babban taro karo na 18 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jam'iyyar za ta kara mai da hankali wajen yaki da matsalolin cin hanci da rashawa, kuma za ta fitar da sabbin matakan yaki da matsalar daga dukkan fannoni. Yanzu babban kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin yana tsara wasu muhimman matakan yaki da kuma yin rigakafin wanzuwar matsalolin cin hanci da rashawa tsakanin shekarar ta 2013 zuwa 2017, inda za ta yi kokarin kyautata tsarin ilmantarwa, yin rigakafi, sa ido da kuma hukuncin da za a yanke kan matsalolin cin hanci da rashawa.

"Za mu kara yin kokari kan yadda za a kyautata harkokin tattalin arziki dana kasuwanci bisa tsarin gurguzu, shimfida harkokin siyasa bisa tafarkin gurguzu, ta yadda za a iya kara sa ido kan jami'an da ke aiki a matakai daban daban na gwamnati, ta yadda za su gudanar da ayyukansu a bayyane domin a samu saukin yaki da kuma rigakafin aikata matsalolin cin hanci da rashawa bisa babban shirin da za a fitar a yayin wannan babban taro karo na 18 na wakilan jam'iyyar, ta yadda za a iya kawar da yanayin aukuwar cin hanci da rashawa."

A yayin da kasar Sin take dada aiwatar da manufar bude kofa da yin gyare-gyare cikin shekaru 30 da suka gabata, an fi sa lura da kuma nuna fatansu kan yadda za a yi gyare-gyare kan tsarin siyasa na kasar Sin. Game da wannan batu, Mr. Cai Mingzhao, kakakin wannan babban taro ya ba da amsa cewa, "Babbar ka'idar da za mu bi lokacin da muke kokarin yin gyare-gyare kan tsarin siyasa ita ce, za mu ci gaba da bin tsarin gurguzu dake dacewa da yanayin da ake ciki a nan kasar Sin a inuwar shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jama'a su ne suke da ikon mulkin kasar, kuma za mu tafiyar da ikon mulkin kasar Sin bisa doka, ta yadda za a iya tabbatar da ganin jama'a sun samu ikon mulkin kasar, kara karfin jam'iyyar da kasarmu. Sannan za a ci gaba da tsayawa da kuma kyautata tsarin babban taron wakilan jama'a, da tsarin siyasa na tattaunawa tsakanin jam'iyyun siyasa daban daban a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Bugu da kari, za a ci gaba da yin amfani da kuma kyautata tsarin tafiyar da harkokinsu da kansu a yankunan da kananan kabilu suke zama, da kuma a kananan hukumomin kasar. (Sanusi Chen, Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China