A gabannin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da za a bude a ranar 8 ga wata, wakilinmu da ke Abuja tarayyar Nijeriya Dan Ladi ya samu damar yin tattaunawa da Sulaiman Mohammed, shugaban sashen nazarin harkokin zaman al'umma a jami'ar Abuja, dangane da yadda jam'iyyar kwaminis da ke mulki a kasar Sin take gudanar da mulkinta da kuma alkiblar neman ci gaba ta hanyar kimiyya da take bi. Ga yadda hirar tasu ta kasance.