in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron share fagen babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18
2012-11-07 17:57:42 cri

An gudanar da taron share fagen babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a ranar 7 ga wata da yamma a babban dakin taron jama'ar kasar Sin, inda shugaban kasar Hu Jintao ya shugabanci taron.

A gun taron, an zartas da jerin sunayen membobi 22 na kwamitin yin bincike kan iznin wakilai masu halartar babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tare da jerin sunayen tawagar shugabannin babban taron dake kunshi da jami'ai 247. Kana an amince da Xi Jinping ya zama babban sakataren babban taron a wannan karo, da kuma yadda aka kafa tsarin sakatariyar da za ta tafiyar da harkokin babban taro a wannan karo.

Ban da wannan kuma, an zartas da muhimman abubuwan da za a tattauna a babban taron a wannan karo, wato sauraron rahoton da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar karo na 17 ya gabatar, yin bincike kan rahoton kwamitin ladabtarwa na tsakiya na kasar karo na 17, zartas da sabbin ka'idojin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka yiwa gyara, zaben kwmaitin tsakiya na jam'iyyar karo na 18 tare da babban kwamitin ladabtarwa karo na 18. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China