in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis na Sin karo na 18 a ranar 8 ga watan Nuwanba
2012-11-07 17:21:06 cri

Yau ranar 7 ga wata, kakakin kula da harkokin watsa labaru na babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis na kasar Sin karo na 18 Cai Mingzhao ya sanar da cewa, za a bude taron da karfe 9 na safiyar ranar 8 ga wata a babban dakin taron jama'ar kasar dake nan birnin Beijing, kuma za a shafe kwanaki 7 ana gudanar da taron wato tun daga ranar 8 zuwa 14 ga wata.

Cai Mingzhao ya ce, an gudanar da taron share fagen babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a ranar 7 ga wata da yamma, inda aka amince Xi Jinping ya zama babban sakataren babban taron a wannan karo. A wannan rana da karfe 4 da rabi na yamma, cibiyar watsa labaru ta babban taron ta gudanar da taron manema labaru a babban dakin taron jama'ar kasar Sin, inda 'yan jarida na gida da waje kimanin dari 6 suka halarci taron. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China