in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kare aniyarta ta kiyaye zaman lafiya a duniya
2012-11-06 19:34:05 cri






A ganin masu lura da al'amuran soja, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu manyan sauye-sauye ga yanayin tsaro a duniya tun bayan da aka fara yakar 'yan ta'adda a shekarar 2001. Duk da cewa cikin shekarun 10 da suka wuce, an fuskanci rikici da tashin hankali a wasu sassan duniya, amma al'ummar kasar Sin sun kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Bin manufar tsaron kanta shi ne alkawarin da rundunar sojojin kasar Sin ta dauka ga jama'ar kasar da na duniya. Baya ga haka, rundunar sojojin kasar Sin ta yi kokarin raya harkokin zamani, har ma a kwanan baya, ta kaddamar da jerin wasu makamai da na'urorin soja na zamani, abin da ya jawo tambayoyin kasa da kasa a game da karfin da rundunar ke da shi da kuma manufar da take aiwatarwa. Domin amsa wadannan tambayoyin, a ranar 5 ga wata, mataimakin babban hafsan hafsoshin rundunar sojojin kasar Sin, Laftana Janar Qi Jianguo ya yi bayani a nan birnin Beijing dangane da halin tsaro da ake ciki a shiyyar, inda ya ce,"A zamanin da muke ciki, kowace kasa in dai tana son samun ci gaban kanta, dole sai ta bar sauran kasashe su nemi ci gabansu. Sa'an nan, in dai tana son tabbatar da tsaronta, dole sai ta bar sauran kasashe su tabbatar da tsaron kansu. Baya ga haka, in dai har tana son jin dadi, dole sai ta bar saura su ji dadi. Ba za mu iya samun moriyar juna da kiyaye kwanciyar hankali ba, sai idan mun hada kanmu."

A gabannin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis da ke mulki a kasar Sin a karo na 18 da za a bude ba da jimawa ba, an dauki wannan furuci a matsayin manufar samun amincewa da juna da moriyar juna da zaman daidai wadai da da juna da kuma hadin gwiwa da juna da rundunar sojojin kasar Sin za ta ci gaba da bi.

Wanda yake son sauke nauyin da ke bisa wuyansa, dole sai ya samu kwarewar yinsa. Don haka, a gun taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 16 da aka gudanar a shekarar 2002, an gabatar da manufar raya harkokin soja na zamani, abin da ya sa cikin shekaru 10 da suka wuce, an yi watsi da wasu nau'o'in soji na gargajiya da dama, sa'an nan, an fitar da jerin wasu sabbin nau'o'in soji na zamani.

A yayin bikin duba faretin soja da aka gudanar a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2009 domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, an nuna jerin wasu sabbin makamai na zamani da kasar Sin ta kera da kanta a babban filin Tian'anmen da ke tsakiyar birnin Beijing, wadanda suka nuna sabbin nasarorin da kasar Sin ta cimma ta fannin raya na'urorin soja.

A ranar 25 ga watan Satumba na shekarar 2012, kasar Sin ta kaddamar da wani babban jirgin ruwan yaki mai daukar jiragen saman yaki, abin da ya kawo karshen rashin samun irin wannan jirgi ga sojojin kasar Sin. Kanar Li Li, wata forfesa a jami'ar koyon harkokin tsaron kasa ta nuna cewa, yadda kasar Sin ta fitar da jerin wasu muhimman makamai ya shaida cewa, rundunar sojojin kasar Sin ta samu babban ci gaba kan wasu muhimman fasahohi. Kanar Li Li tana mai cewa,"wasu abubuwan da ba mu iya gwajinsu ba amma yanzu muna iya yi bisa wannan babban jirgin ruwan yaki, al'amarin da ke da muhimmanci sosai ga bunkasa makamai da na'urorin soja na zamani a kasar Sin. Har wa yau, muna kuma da sabon jirgin ruwan fada dake bacewa a kan ruwa da kuma wani sabon jirgin ruwan yaki na zamani, wadanda dukkansu suka shaida babban ci gaban da muka samu ta wannan fanni."

Amma duk da haka, a yayin da kasar Sin take raya makamai da na'urorin soja na zamani, wasu kasashe sun fara shakkar barazanar da sojojin kasar Sin ke iya kawowa. Domin kara bayyana wa duniya halin da rundunar sojin kasar Sin ke ciki, tun shekarar 2002, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardun bayani biyar a kan harkokin tsaro na kasar. Ban da haka, ta kuma kafa tsarin gudanar da taron manema labarai, don bayyana wasu abubuwan da ke jawo hankalin kasa da kasa cikin lokaci.

Cikin shekaru 10 da suka wuce, rundunar sojin kasar Sin ta kuma kara fitowa a fagen duniya, wadda take kokarin shiga harkokin duniya tare da bunkasa dangantaka da takwarorinta na kasa da kasa. Kawo yanzu, rundunar ta kulla hulda da rundunonin sojojin kasashe sama da 150, tana kuma gudanar da shawarwari da sassan tsaro da rundunonin sojojin na kasashe 22. Baya ga haka, ta kuma hada kai da rundunonin sojin kasashe sama da 30 wadanda suka gudanar da atisayen soji sama da 50. Cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta tura ma'aikata kimanin dubu 20 domin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, don haka, ta kasance kasar da ta fi yawan tura ma'aikatan kiyaye zaman lafiya a cikin kwamitin sulhu. A sa'i daya, kasar Sin ta kuma yi kokarin shiga harkokin ba da kariya a jiragen ruwa a mashigin teku na Aden da kuma Somaliya.

Liang Guanglie, ministan tsaron kasar Sin ya ce, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka a kan bin manufar tsaron kanta ba tare da kawo barazana ga kowace kasa ba."Akwai babban bambanci a tsakanin kasar Sin da kasashe masu ci gaba ta fannin matsayin da suka kai a wajen makamai da na'urorin aikin soja. Kasar Sin ta bunkasa wasu makamai bisa ga bukatu na tsaron kanta. Ba domin wata kasa muke bunkasa makamai ba, kuma ba za mu kawo barazana ga kowace kasa ba."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China