in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan aka fahimci jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, za a iya fahimtar kasar Sin
2012-11-05 17:34:17 cri






Nan ba da dadewa ba, za a shirya babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18, don haka hankalin duk duniya ya karkata ga birnin Beijing. A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta bi manufar bude kofa ga kasashen waje, kuma ta kafa hanyoyin mu'amala da kungiyoyi da jam'iyyun siyasa kimanin 600 da suka fito daga kasashe sama da 160. Sabo da jam'iyyun siyasar na da bambancin yanayi da bambamcin tsarin gudanarwa, sun yi shawarwari bisa sahihiyar zuciya, ta hakan ne, suka kara fahimtar juna da kokarin lalubo bakin zaren yadda za a yi hadin gwiwa tsakaninsu, haka kuma jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kara samun amincewa daga kasashen duniya.

Daga ranar 2 zuwa ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 2010, shugaban sashen kula da harkokin tuntubar kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Wang Jiarui, da jiga-jigan siyasa na jam'iyyun Republic da demukoradiyya na Amurka, sun shugabanci shawarwari tsakanin manyan jami'an jam'iyyun siyasa na kasashen Sin da Amurka, sabo da wannan lokaci ya zama wata guda kawai kafin shugaban kasar Sin ya kai ziyara zuwa kasar Amurka a farkon shekarar 2011, hakan ya jawo hankalin kasashen duniya sosai, kuma kafofin yada labaru na kasashen Sin da Amurka sun mai da hankali sosai game da batun.

A hakika, an yi shawarwari tsakanin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun siyasa biyu na Amurka ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba. A watan Maris na shekarar 2010, an yi shawarwari tsakanin jam'iyyun siyasa na kasashen Sin da Amurka karo na farko a nan birnin Beijing, kuma jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta fara yin mu'amala bisa wani tsari na kullum, tare da jam'iyyun siyasa na Republic da Demokuradiyya na kasar Amurka, wannan shi ma ya kafa wani sabon dandali ga jam'iyyun siyasa da jami'an gwamnatocin kasashen biyu, da za su kara fahimtar juna da amincewa, juna bisa manyan tsare-tsare, da kara raya huldar da ke tsakaninsu. Game da wannan, yayin da kakakin sashen kula da tuntubar kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Huang Huaguang ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, "An shirya taron koli tsakanin jam'iyyun siyasa na kasashen Sin da Amurka har sau 4, bayan da aka kammala babban taron wakilan JKS karo na 18, haka kuma bayan babban zaben kasar Amurka, shugaban sashen kula da tuntubar kasashen waje na kwamintin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Wang Jiarui, zai shugabanci wata tawaga zuwa kasar Amurka, don musayar ra'ayi tare da jam'iyyun kasar Amurka guda biyu, kuma wannan tsari ya zama mai kyau, sabo da a kan gudanar da tsarin canja jam'iyyar da ke gudanar da mulki a wasu kasashe, idan wata jam'iyyar ta sauka daga mukamin jagoranci, kuma jam'iyyar adawa ta hau karagar mulki, ba zamu samu matsala wajen kula da huldar dake tsakanin bangarori 2 ba, domin da ma mu kan yi kokarin mu'amala da wannan jam'iyya."

A watan Yuli na shekarar 2011, an balle Sudan ta Kudu daga kasar Sudan, kasar da a baya ta fi ko wace girma a kasashen dake Afrika, inda Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai, amma kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun ci gaba da ja-in-ja game da batutuwan shata iyakokin kasashen biyu da batun man fetur da dai sauransu, Huang Huaguang ya ce, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta sa kaimi domin yin shawarwari da jam'iyyun siyasa da ke gudanar da jagoranci a Sudan, da Sudan ta Kudu, don cimma matsayar yin shawarwari tsakaninsu, ya ce, "Mun kafa dangantaka mai kyau tare da jam'iyyun da ke da gudanar mulki a kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, kuma ta wannan hanya ne, muke fatan ci gaba da kokarin aiki, tare da share fagen yin shawarwari a tsakaninsu, don lalubo bakin zaren warware rikicin da ke tsakaninsu.

Huang Huaguang ya ce, yayin da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke tuntubar kasashen waje, ta bi manufar bude kofa ga kasashen waje cikin sahihiyar zuciya, kamar yadda wani jami'in jam'iyyar FDP na kasar Jamus Lape Racita ya bayyana cewa, "Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jam'iyya ce da ta gudanar da ayyuka a bayyane, kuma ta yi mu'amala da jam'iyyun kasashen duniya da ke da bambancin ra'ayi a siyasance, matakin da ya inganta fahimtar juna tsakanin al'ummar kasashen duniya. A cikin 'yan shekarun nan, mun yi mu'amala da kasar Sin wajen harkokin siyasa, hatta ma, yayin da aka tabo maganar da ke da sabani tsakaninmu, mu ma muna iya bayyana matsayin da muke kai game da batun.

Game da makomar aikin tuntubar kasashen waje na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kakakin sashen kula da harkokin tuntubar kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Huang Huaguang ya bayyana cewa, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta kara yin mu'amala da kasashen waje game da fannoni daban daban, don inganta tuntuba tsakaninta da sauran kasashen duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China