in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da cikakken zama na 7 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 17
2012-11-04 19:23:24 cri

An gudanar da cikakken zama na 7 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 17 tun ranar 1 zuwa ta 4 ga wata a nan birnin Beijing, kwamitin hukumar harkokin siyasa ne ya shugabanci taron, kana babban sakataren kwamitin Hu Jintao ya yi jawabi yayin taron.

A gun taron, an tsaida kudurin gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a ranar 8 ga wata. Kana an saurari tare da tattauna rahoton da Hu Jintao ya gabatar bisa bukatun hukumar harkokin siyasa. A gun taron, an nuna yabo ga hukumar harkokin siyasa domin ta gudanar da ayyuka yadda ya kamata bayan cikakken zama na 6 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 17, kuma an takaita ayyukan da aka gudanar a shekaru 5 da suka gabata bayan da aka gudanar da taron jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 17.

Ban da wannan kuma, an yi bincike kan halin da ake ciki a kasar Sin, da tattauna yadda za a bunkasa Sin mai halayen musamman na gurguzu da kuma raya sha'anin jam'iyyar kwaminis ta kasar don share fagen gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China