in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Na koma kasar Sin, sabo da na yi imani game da makomar kasar"-labarin Chen Pengfei da harkokin tattalin arzikin kasar
2012-11-02 17:37:15 cri






A cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da aka yi ta kokarin raya tattalin arzikin kasar, a kan samu kalubale da dama, amma kasar Sin ta kan tinkarar irin kalubalen da ke gabanta, kuma a daidai wannan lokaci, kwarin gwiwa da aka nuna wa tattalin arzikin kasar Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar matsala. A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta zama gamayyar tattalin arziki ta biyu a duniya, kuma tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da habaka cikin armashi, manyan shugabannin kasar Sin ko jama'a sun nuna kwarin gwiwa game da makomar kasar.

A wurin da ake fi samun masana'antun fasahohin sadarwa da dama da ke nan birnin Beijing, akwai wata karamar masana'antar da ke cikin wadannan manyan gine-ginen masana'atu, kuma wannan masana'antar ta shahara ne sakamakon da fasahohin zamani 3D da ta kirkiro, kuma wani basine Chen Pengfei da abokinsa suka bude wannan masana'anta da kansu. A matsayinsa na wani manajan kamfanin, Mr. Chen mai shekaru 30 yana shan aiki sosai. Idan aka waiwaya baya, a shekarar 2004, Mr. Chen ya yi shirin zuwa karatu a kasar Amurka, kamar sauran abokan karatunsa, sun sa burinsu zuwa kasar Amurka. A karshe dai, burinsa ya cika, ya samu damar yin karatu a jami'ar California da ke kasar Amurka, kuma ya yi karatu a fannin injiniyanci na Lantarki a jami'ar. Yayin da Mr. Chen yake karatu a can, ya yi tunani game da makomarsa. Bayan da ya kwatanta yanayin tattalin arziki da ake ciki a kasashen Amurka da Sin, ya yanke shawarar ci gaba da aiki a kasar Amurka, inda aka fi wadata wajen sana'ar injiniyancin lantarki. Ya ce, "Bayan da na isa kasar Amurka, na saba da yanayin da ake ciki a wurin, kuma ina tsammani zan yi aiki a can, sabo da game da wannan sana'ar tamu, matsakaitan da kananan kamfanoninmu da ke kasar Amurka suna da kyau, kuma yayin da tattalin arzikin Amurka na da kyau, jama'a sun fi son bude sana'o'insu, kuma a cikin manyan kamfanoni, ake ba da albashi mai kyau."

Bayan da Chen Pengfei ya kammala karatu, ya samu aiki a wani babban kamfanin fasahohin zamani na kasar Amurka dake sahon gaba a duk kasashen duniya, kuma nan take ya zama manajan kamfanin. Ko da yake, yana kasar Amurka, amma Chen Pengfei ya ci gaba da mai da hankali sosai game da bunkasuwar kasar Sin. Yayin da ya yi aiki a kasar Amurka, ya yi la'akari da cewa, kasar Sin ta gaggauta samun bunkasuwa cikin hanzari, kuma manyan masana'antu na kasashen Amurka da Turai su ma sun zura ido sosai game da kasuwannin kasar Sin, har ma wasu masana'antu sun kara saka jari a kasar Sin, ban da wannan kuma, wasu masana'antu sun kafa cibiyoyin nazari a biranen Beijing da Shanghai na kasar Sin. Mataimakin shugaban bankin Citibank William Rhodes ya taba bayyana ra'ayinsa game da saka jari a cikin kasuwannin kasar Sin, ya ce,

"Na gano cewa, an samu manyan canje-canje a kasar Sin, ba ma kawai a yankunan da ke bakin teku ba, hadda ma a wuraren da ke yammacin kasar, an samu babban canji ne matuka, musamman ma a fannin habakar kirkire-kirkire."

Yayin da masu saka jari na kasashen waje suka sa ido sosai kan tattalin arzikin kasar Sin, Chen Pengfei shi ma ya yi tunani sosai game da batun, ko zai koma kasar Sin don raya harkokinsa? Amma ba zato, rikicin kudi na kasashen duniya ya bullo kai a kasashen duniya, Chen Pengfei ya gane wa idonsa irin tasirin da rikicin kudi na duniya ya kawo wa tattalin arziki na kasar Amurka, amma, a hakika, rikicin kudi na duniya shi ma ya kawo mummunan tasiri kan tattalin arzikin Sin, an samu tafiyar hawainiya wajen habaka tattalin arzikin kasar. Domin tinkarar rikicin kudi na duniya, da ba da tabbaci wajen raya tattalin arziki da kyau kuma cikin hanzari, gwamnatin Sin ta dauki matakai da dama cikinsu har ta gabatar da wani shirin farfado da tattalin arziki na saka jari da yawansa ya kai RMB biliyan 4000, ban da wannan kuma, shugabannin kasar Sin sun jaddada a gida da waje har sau da dama, kuma sun bayyana wa gwamnati da jama'a na kasar da su kara nuna kwarin gwiwa wajen tinkarar rikicin kudi na duniya, kuma lamarin ba ma kawai, ya karfafa zukatan jama'a ba, kana kuma ya sa tattalin arzikin duniya ya samu makoma mai haske. Sabo da haka, Chen Pengfei ya tsaida anniyar komawa gida don raya harkokinsa. A shekarar 2008, Chen Pengfei ya dawo kasar Sin, don bude sana'arsa. Haka kuma a shekarar 2010, Chen Pengfei ya yi amfani da fasahohin zamani na 3D don bude sana'arsa, kuma a wannan shekara ya kafa kamfaninsa tare da wasu abokai.

Chen Pengfei ya ce, ya yi imani sosai game da makomar kamfaninsa, sabo da ya yi imani sosai game da makomar tattalin arzikin kasar Sin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China