Shugaban jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya, Alhaji Bamanga Tukur ya ce, kamar a kasar Sin, Jam'iyyar kwaminis ta Sin har kullum tana kokari sosai wajen kara kyautata zaman rayuwar jama'a, haka ma Jam'iyyar PDP tana gudanar da harkokin mulki a Nijeriya yadda ya kamata, sabo da haka tana son hada kai da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.
Shugaban na PDP ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da wakilin sashen hausa na CRI a ran 1 ga wata a Abuja, inda ya ce PDP da JKS za su kara yin cudanya da juna
Alhaji Bamanga Tukur ya kara da cewa, a wannan wata za a gudanar da babban taro karo na 18 na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma yana fatan za a kara yin mu'amala tsakanin jam'iyyun biyu domin taimakawa jama'ar bangarorin biyu.(Danladi, wakilin CRI daga Abuja, Nijeriya)