in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta yi kokarin yin kwaskwarima don samun ci gaba tare da sauran kasashen duniyia baki daya
2012-11-01 16:39:34 cri






Bayan da kasar Sin ta gudanar da manufar bude kofa da yin kwaskwarima a shekarar 1978, tunanin yin kwaskwarima ya samu yaduwa a dukkan kasar Sin. A cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, kasar Sin ta yi kwaskwarima sosai yayin da ake raya kasar, kamar kwaskwarima ga tsarin tattalin arziki, kauyuka da birane, kamfanoni mallakar kasar Sin, harkokin kiwon lafiya, bada ilmi, hada-hadar kudi da dai sauransu, wadanda suka kawo babban canji ga kasar Sin a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Kamar yadda firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya ce, yin kwaskwarima ya zama tushen inganta tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin. Don haka bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ta zama abin mamaki a fadin duniya. Yanzu ga cikakken bayani da …. ya kawo mana:

Sakamakon kwaskwarimar da kasar Sin ta aiwatar, ya sa Sin ta samu babban ci gaba a fannin tattalin arziki a shekaru fiye da 20 da suka wuce, alamarin da ya baiwa duniya mamaki matuka. Amma a gun dandalin tattaunawa kan zuba jari ga sana'ar dab'i a tsakanin Sin da Ingila da aka gudanar a birnin London a kwanakin baya, wani masanin tattalin arziki daga kasar Sin Li Yining ya nuna cewa, sakamakon wasu nasarori da aka samu a fannin tattalin arziki a kasar Sin, tilas ne a ci gaba da yin wannan kwaskwarima. A halin yanzu, kwaskwarimar da kasar Sin take yi ba ta shafi kasar kawai ba, har ma ta jawo hankalin duniya baki daya, domin kwaskwarimar da Sin ta yi za ta yi babban tasiri ga dukkan duniya.

Da farko, kasar Sin ta maye gurbin kasar Japan na kasa mafi karfin tattalin arziki na biyu a duniya a shekarar 2010, kana bisa hasashen da asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya yi, watakila kasar Sin za ta zarce kasar Amurka a shekarar 2016 a matsayin kasa ta farko ta duniya a fannin tattalin arziki. Rikicin hada-hadar kudi na duniya bai yi babbar illa ga kasar Sin ba, koda yake karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu kadan a farkon bana, amma wasu kasashen yammacin duniya su nuna damuwa sosai domin raguwar tattalin arzikin Sin za ta kawo illa ga tattalin arzikin duniya.

Hakazalika kasar Sin ita ce kasar dake kan gaba wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kana kasa ta biyu da ta fi shigowa da kayayyaki daga sauran kasashen waje. Sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, ana ganin cewa, watakila za ta zama kasa ta farko da ta fi shigowa da kayayyaki daga kasashen duniya.

Haka kuma, a cikin 'yan shekarun nan, masana'antu da masu saka jari na kasar Sin da dama sun bar kasar, inda suke saka jari a sassan daban daban na kasashen duniya, kuma jarin da kasar Sin ta saka a kasashen duniya ya kawo babban jari ga wasu kasashen duniya, bisa kididdigar da ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Sin ta bayar, an ce, a shekarar 2009, kasar Sin ta zama kasa ta biyar da ta fi saka jari ga kasashen waje, kuma ta dau matsayi na farko cikin kasashe masu tasowa, kana tana matsayi na farko a cikin kasashen da ke wannan yanki.

Haka kuma, duk wadannan nasarorin da Sin ta samu sun sa aikin yin gyare-gyare a kasar ya jawo hankalin duniya, a sa'i daya kuma, gyare-gyaren da za a yi a kasar Sin na da ma'anar musamman ga kasashen duniya.

Game da cinikin kasa da kasa, kasashen duniya sun mai da hankali sosai game da matakan da kasar Sin za ta dauka don gaggauta canja salon raya tattalin arziki, kuma ba za ta dogara ga fitar da kayayyaki don sa kaimi ga raya tattalin arziki ba, kana kuma, kara yawan bukatun sayayya a cikin gida ya haddasa kayayyakin kasashen duniya za su kara iya samun damar shiga kasuwannin kasar Sin, wannan zai taimaka wajen rage gibin cinikin da ke kasancewa tsakanin kasar Sin da kasashen duniya.

Dadin dadawa kuma, matakan da Sin za ta dauka don kyautata dokoki da kafa tsarin doka a kasar, da bayyane manufofin da za ta aiwatar a bayyane, da kare ikon mallakar fasaha su ma sun jawo hankalin masu saka jari na kasashen waje sosai.

Ban da wannan kuma, kasashen duniya sun yi la'akari da cewa, yayin da tattalin arzikin Sin ya samu habaka cikin gaggawa, abin da ya sa kaimi da kara bukatun makamashi a duniya, haka kuma ya kawo babban matsin lamba game da batun kiyaye muhalli, sabili da haka, a halin da ake ciki yanzu, Sin ta jaddada daukar matakan canja salon raya tattalin arziki, lamarin da ya kuma samu karbuwa daga kasashen duniya. A matsayinta ta babbar kasar da ke da al'umma da yawansu ya kai kashi 1 cikin 5 na al'ummar kasashen duniya, duk wani kokarin da kasar Sin ta yi zai kawo babbar moriya ga kasashen duniya.

Amma, abin da ya fi jawo hankalin kasashen duniya, shi ne, zaman lafiya wajen tafiyar da harkokin siyasa da zaman jituwa a tsarin zamantakewar al'umma, yayin da kasashen duniya suke sa ran ganin samun gyare-gyare ta fuskar tsarin tattalin arziki na kasar Sin, su ma suna fatan za a samu sakamako mai tasiri a tsarin siyasa na kasar Sin.

A hakika dai, bayan da matsayin tattalin arziki na kasar Sin ya ci gaba da haura na sauran kasashen duniya, gyare-gyaren da kasar Sin ke aiwatarwa na da ma'anar musamman ga kasashen duniya, kuma kasar Sin za ta kokarta samun moriyar juna da kasashen duniya, yayin da take karfafa aikin yin gyare-gyare a kasar. (Zainab+Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China