in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ikon jefa kuri'u na jama'ar kasar Sin
2012-10-31 15:55:54 cri






Tsarin jefa kuri'u shi ne tushen demokuradiyya, ikon jefa kuri'u tushe ne na ikon siyasa na jama'a. A shekarar 2004 da kuma shekarar 2010, hukumar tsara dokokin kasar Sin ta gyara dokar zaben kasar sau biyu. Bayan aiwatar da wadannan gyare-gyare, jama'ar kasar Sin sun samu damar jefa kuri'u cikin adalci, kana jama'a sun fi kara sanin halin 'yan takara a zaben majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma yawan wakilan daga bangaren fararen hula yana karuwa. Wannan ya bayyana cewa, an kara tabbatar da ikon demokuradiyya na jama'ar kasar Sin a shekaru 10 da suka wuce.

"Bisa tunanina, wakilai su ne mutanen da suke gudanar da ayyuka domin taimakawa jama'a cikin adalci. Su kan je gonarmu don yin bincike kan ko muna da isasshen kudi, ko muna bukatar taimako ko a'a. Idan ba su yi hira da mu ba, ba za mu san ko suna gudanar da ayyukansu ko a'a. Suna iya bayyana bukatunmu a madadinmu, musamman a fannin rayuwar jama'a, kamar bada ilmi, kiwon lafiya, raya birane da sauransu. Kana su kan tattara ra'ayoyinmu."

Bisa kundin tsarin mulkin kasar Sin, jama'a suna mallakar dukkan ikon kasar, sun yi amfani da ikon kasar ta hanyar majalisar wakilan jama'ar kasar. Tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin shi ne tushen tsarin siyasar kasar Sin. Kana ikon jefa kuri'u muhimmin iko ne na wannan tsari, wanda ya shafi bayyana ra'ayoyin jama'a da kuma tsarin jami'an gwamnatoci na mataki daban daban, don haka shi ne tushen tsarin demokuradiyya. Shekarar 2011 shi ne karo na farko da kasar Sin ta zabi wakilan jama'a daga birane da kauyuka da yawansu ba shi da bambanci. Wannan ne karo na farko da manoman kasar Sin suka samu ikon shiga takara a zaben majalisar wakilan jama'ar kasar wanda yayi daidai da ikon na mazauna birane. Don haka, an kara sa kaimi ga jama'a daga kauyuka da birane da suka shiga harkokin siyasar kasar.

Yayin da ake gudanar da zaben wakilan jama'a a garin Yeping dake yankin Ruijin na lardin Jiangxi, wani mutum ya tambayi wata 'yar takara game da yadda za ta yi idan ya zama wakilin jama'a. Wannan 'yar takara ta bayyana cewa,"Idan na zama wakiliyar jama'a, zan dora muhimmanci game da yin bincike kan zuba jari, koyar da fasahohi, kafa sabbin kungiyoyin tattalin arziki a fannin aikin gona bisa halin da ake ciki a garin Yeping, kuma zan gabatar da rahoto a gun taron wakilan jama'ar garin."

A wasu shekaru da suka gabata, kasar Sin ta gyara dokar zabe sau biyu don kyautata ka'idojin ganawa a tsakanin 'yan takara da masu jefa kuri'u. Bisa ka'idojin, hukumomin zaben sassan kasar Sin sun shirya ganawa a tsakanin 'yan takara da masu jefa kuri'u. Wannan ya baiwa jama'a sun fi damar sanin halin 'yan takara kai tsaye, kuma sun fi sauki wajen zaben wakilai.

A wadannan shekaru, yawan wakilan jama'a da suka zo daga bangaren fararen hula yana karuwa. A ganin masana, an zabi wakilan jama'a ba bisa takardar karatu da matsayinsu kawai ba, abu mafi muhimmanci shi ne ko suna iya bayyana ra'ayoyin jama'a da burinsu ko a'a, kana sun gudanar da ayyukan kasa a madadin jama'a. Bayan da aka kyautata tsarin zabe, wakilai su fi samun wakilci a tsakanin jama'a, kana sun kara sa lura kan ra'ayoyin jama'a.

Game da canjin da aka samu bayan da aka gyara dokar zabe, shugaban sashen ilmin dokoki na jami'ar jama'ar kasar Sin Han Dayuan ya bayyana cewa,"An bayyana batun adalci yayin da ake gudanar da zaben kasar, wannan zai sa masu jefa kuri'u su kara azama ga bunkasuwar tsarin demokuradiyyar kasar Sin, kuma za a inganta tsarin zaben kasar Sin yadda ya kamata." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China