in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da suka fito daga sabbin fannoni
2012-10-30 18:27:50 cri






Kasar Sin ta samu manyan sauye-sauye sakamakon manufar da take gudanarwa na yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, hakan dai yasa aka bullo da wasu sabbin fannoni da suka hada da masu masana'antu na zaman kansu, kwararru dake aiki a kamfanonin kasashen waje da ke zuba jari a kasar, da masu sana'a da sauransu.

Tun bayan da aka gabatar da shigar da fitattu a sabbin fannoni cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis da ke mulki a kasar karo na 16, 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da suka fito daga sabbin fannoni suna ta karuwa, hakan yasa aka soma ajiye sunayen fitattu daga cikinsu a cikin jerin wakilan babban taron wakilan. A shekarar da muke ciki, aka zabi mutane guda 27 daga sabbin fannoni don halartar babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis karo na 18, inda Li Denghai,wani babban attajiri, da Zhou Mingjue, akanta da aka yi rajista, suka fi jawo hankalin jama'a. Yanzu ga cikakken bayanin da Bilkisu ta kawo mana:

Kusan shekaru 30 da suka wuce, babban darektan kamfanin samar da iri na Denghai na lardin Shandong na kasar Sin, Li Denghai ya yi nazari sosai kan wani labarin da ya samu a lokacin. A shekaru 60 na karnin da ya wuce, Li Denghai da ya gama karatu a sakandare ya komo garinsu don soma aikin gona, yadda yake ji abubuwan da yunwa kan haifar ya sa yana son cimma wani buri, wato kokarta kara samar da masara a garinsu, domin dukkan mutanen kauyensu su iya samun isassun abinci. Shi da abokansa sun yi kokarin gwajin noman masara masu aure, har ma yawan masara da suka samu ya ninka sau uku idan aka kwatanta da irin masara na gargajiya. Amma, a lokacin ya samu wani labari cewa, yawan masara da wani kamfanin kasar Amurka mai suna Pioneer ya samar ya ninka 2.5 bisa nasu. Tun daga lokacin kuma, Li Denghai ya soma neman hanyar yin gwaji kan irin masara masu aure, wannan aikin ya raka masa har zuwa yanzu. Li Denghai ya gaya mana cewa,

"A lokacin na yi tsamanin cewa, shugaban kamfanin Pionner, Wallace shi ne manomi na kasar Amurka, ni ma wani manomi ne na kasar Sin, idan jama'ar kasashen waje zasu iya yi wannan abu, mu Sinawa ma zamu iya."

Li Denghai na da labari mai ban mamaki, ko da yake bai taba shiga jami'a ba, amma ya kasance a babban matsayi kamar yadda shugaban kamfanin Pionner, Wallace yake a fannin noman masara, mutanen biyu sun kai matsayin koli na duniya ta fuskar samar da masara ta yanayin zafi da na bazara. A shekaru 80 na karnin da ya wuce, Li Denghai ya kafa wani sashen nazarin masara, a shekarar 2002, ya hada kai da kamfanin samar da iri na Pioneer na kasar Amurka, kuma kanfanin ya cimma nasarar sayar da hannun jari a shekarar 2005, hakan dai Li Denghai ya kasance wani darektan kamfanin sayar da hannun jari da kaddarorinsa ya wuce RMB miliyan 100.

Yanzu, Li Denghai da shekarunsa na haihuwa suka wuce 60 bai taba dakatar da hanyarsa ta cimma sabon buri ba.

"Mun yi girma ne sakamakon horar da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta yi, saboda haka muna fatan taka muhimmiyar rawa kan ci gaban kasarmu. Nan gaba, zan ci gaba da samar da moriyar tattalin arziki na RMB biliyan 100 ga kasarmu ta hanyar nazarin irin masara na wajen mu."

Masu masana'antu dake zaman kansu kamar yadda Li Denghai yake, ana iya samun su da yawa a matsayin wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis da aka shirya a shekarar 2002, yawan wakilan da suka fito daga masu masana'antu na zaman kansu ya kai 7, amma a yayin babban taron karo na 18 da za a shirya a bana ya kai 27, wannan ya nuna cewa, matsayin siyasa na masu masana'antu na zaman kansu ya karu, kuma ikonsu na fada a ji shi ma ya karu sosai.

A cikin wakilan da za su halarci babban taron na bana, akwai wani da ya fi jawo hankalin jama'a, wato Zhou Mingjue, wanda shi kadai ne ya ci nasarar zaben wakili daga cikin akanta da suka nemi ayi ma rajista su dubu 250 na dukkan kasar. Zhou Mingjue, 'dan shekaru 56 a duniya na ganin cewa, akanta da suka yi rajista na fuskantar kalubale kan yadda ba da tabbaci ga raya tattalin arzikin kasar.

"Muna kira ga dukkan al'umma da ta kara fahimtar sana'ar akanta da suka yi rajista, da kuma yin la'akari da samar da wani muhallin zartaswa da ya dace don taimake mu wajen biyan bukatun bunkasuwar tattalin arziki. Kamata ya yi mu samar da kididdiga da bayanai cikin adalci, in ba haka ba, za a samu cikas ga ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata."

Kwararru a sabbin fannoni a yanzu haka na kara taka muhimmiyar rawa kan dandalin siyasa na kasar Sin. A ganin shugaban kungiyar hadin kan kwararru na sabbin fannoni, Han Deyun, an samu wannan yanayi ne sakamakon budewar tunani ta jam'iyyar dake rike da mulki ta kasar Sin, da canzawar ra'ayin da al'umma ke nunawa sabbin fannoni, dukkansu sun nuna sabon ci gaba da kasar Sin ta samu wajen harkokin siyasa irin na demokuradiya. Han ya ce,

"Shigar da kwararru daga sabbin fannoni cikin jam'iyyar dake rike da mulkin kasa, ba kawai ya nuna matsayin da jam'iyyar dake rike da mulkin kasar na amincewa da ra'ayoyi daban daban ba, har ma yana nuna cewa, an riga an mayar da kwararru a sabbin fannoni a matsayin wani muhimmin sashe ne na kara karfin rike mulkin kasa." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China