in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta warware matsalar samar da tsabtataccen ruwan sha ga mazauna karkara milyan 300 kafin shekarar 2015
2012-10-30 15:44:03 cri

A ran 29 ga wata, an gudanar da dandalin manyan jami'an kula da harkokin ruwa na kasar Sin karo na 7 a birnin Beijing, yayin wannan taro, mataimakin direktan cibiyar bunkasa noman rani da samar da ruwan sha Yan Guanyu, ya bayyana cewa, a tsakanin shekara ta 2011 da 2015, kasar Sin za ta kara mai da hankali kan aikin samar da ruwan sha a kauyuka, ta yadda za a cimma burin gina sabbin kauyuka na gurguzu, kana za a iya warware matsalar samar da ruwan sha mai tsabta ga mazauna kauyuka milyan 298, da kuma dalibai da malamai na makarantu dubu 114 a karkara.

A tsakanin shekara ta 2011 da ta 2015, kasar Sin za ta kara zuba jari domin tabbatar da ayyukan samar da lantarki, da wurare tare kuma da rage harajin da za a buga yayin da ake kokarin kara karfafa ayyukan binciken ingancin ruwan sha a gundumomi daban daban na kasar, a karshe dai, mazauna karkara za su more daga wajensu cikin dogon lokaci.

Bisa labarin da aka samu, an ce, tun daga shekarar 2002, har zuwa yanzu, a cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, gaba daya yawan kudin da Sin ta zuba kan wannan babban aiki ya kai yuan bilyan 178.6, inda ta warware matsalar samun ruwan sha mai tsabta ga mazauna kauyuka da kuma dalibai da malamai na makarantun kauyuka milyan 326, wanda ke nuna adadin mutanen kauyuka da ke cin moriyar ayyukan samar da ruwa ya karu daga kashi 38 bisa dari a shakarar 2004, zuwa kashi 63 bisa dari a shekarar 2011.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China