in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu ci gaba mai kyau wajen yin gyare-gyare a fannin jiyya
2012-10-30 11:17:52 cri

Jami'in kula da harkokin kiwon lafiya da tattalin arziki na bankin duniya John Langenbrunner ya ba da bayani kwanan baya cewa, tun lokacin da Sin ta sanar da yin gyare-gyare kan tsarin kiwon lafiya da ba da magani a shekarar 2009, kasar ta samu ci gaba mai armashi.

A cikin bayaninsa, ya ce, a cikin shekaru 3 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta zuba jarin da ya kai kimanin dala biliyan 125 a wannan fannin, wanda ya taimaka wajen samarwa Sinawa da yawansu ya kai kashi 95 bisa 100 inshorar lafiya. Abin da ya fi girgiza mutane shi ne, yawan mazaunan kauyukan Sin da suka soyo inshorar lafiya cikin shekaru 10 da suka gabata ya karu har ya kai miliyan 800.

John Langenbrunner ya ce, ya zuwa yanzu Sin ta fahimci cewa, ya kamata, ta mai da hankali kan raya tattalin arziki a fannoni daban-daban a maimakon ba da muhimmanci kan samar da kayayyaki kawai. Samarwa karin mutane inshorar zai taimakawa wadannan mutane wajen sayen karin kayayyaki, ta yadda za a habaka bukatun cikin gida. Kuma ya jaddada cewa, ci gaban da Sin ta samu a wannan fanni ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki cikin daidaici. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China