in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labaran 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da suka fito daga kananan kabilu
2012-10-29 17:36:36 cri








Ba da jimawa ba za a kira babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis da ke mulki a kasar Sin karo na 18 a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar, inda wakilan 'yan jam'iyyar sama da 2200 da aka zaba daga 'yan jam'iyyar sama da miliyan 80 za su hadu su tattauna jerin muhimman abubuwan da ke shafar makomar jam'iyyar da kuma makomar kasar ta Sin. Sabo da haka, wakilan 'yan jam'iyyar da ke daukar babban nauyi na jan hankalin al'umma, kuma Wei Dengdian, Memetcan Umer, Hong Hanying na daga cikinsu, wadanda kuma 'yan kananan kabilu ne na kasar.

Wei Dengdian ya fito ne daga wani kauyen da ake kira Kanzicun na 'yan kabilar Hui. A shekarar 1975, 'yan kauyen sun zabi Wei Dengdian a matsayin sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke wannan kauye, daga nan kuma Wei Dengdian ya shafe tsawon shekaru 37 yana kan mukamin. A yanzu haka Wei Dengdian wanda ke da shekaru kusan 60 a duniya yana da wani buri na ganin 'yan kauyensu sun samu jin dadin zaman rayuwa, kamar yadda ya ce mana,"A ganina, ya kamata a hada kan 'yan kauyenmu don su yi kokari ta fuskar gyaran yanayin kauyenmu, domin kowa ya ji dadin zaman rayuwarsa, wannan ne babban burina. Domin cimma wannan buri kuma, kullum ina tunani a kan yadda zan ba da gudummawata wajen raya wannan kauye."

Cikin shekaru 37 da suka wuce, Wei Dengdian ya hada kan 'yan kauyen nasu domin su shimfida hanyoyi da samar da wutar lantarki da ruwan sha, har ma an samu wadata a wannan kauyen da da yake fama da talauci. A watan Yuni na wannan shekara, an zabi Wei Dengdian a matsayin wakilin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A cewar Wei Dengdian, yana wakiltar 'yan kananan kabilu da ke da zama a karkara, kuma zai yi kokarin sauke nauyin da ke wuyansa ta hanyar isar da sakon al'ummarsa a babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da za a kira.

Memetcan Umer shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin kauyen Bulikai da ke jihar Xinjiang a arewa maso yammacin kasar Sin, kauyen da 'yan kabilun Uygur, Kazak da na Han ke zaune.

A cewar Memetcan, kasancewarsa kauyen da 'yan kabilu da dama ke zaune tare, inganta hadin kan kabilu na da muhimmancin gaske ta fuskar raya shiyyar. Memetcan ya ce,"kamata ya yi mu yi kokarin kiyaye hadin kan kabilu kamar yadda muke kiyaye idanunmu. In ba hadin kan kabilu, babu kwanciyar hankalin al'umma, kuma in dai babu kwanciyar hankalin al'umma, ba za a iya samun ci gaban al'ummar ba. Har wa yau, idan babu ci gaban al'umma, jama'a ba za su ji dadin rayuwa ba."

Bugu da kari, Memetcan ya jagoranci 'yan kauyen wajen kokarin shigo da fasahohin zamani don raya ayyukan gona da kiwon dabbobi, har ma yanzu haka kauyen ya yi suna a wajen ci gaba. A game da yadda aka zabe shi a matsayin wakilin 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Memetcan ya ce, kawai ya yi abin da ya kamata ya yi ne, kuma zai kara kokari a nan gaba.

Hong Hanying wadda ke da shekaru 47 a duniya 'yar kabilar Xibo ce da aka haifa a jihar Xinjiang, kuma a yanzu haka tana aiki ne a jami'ar koyon maganin gargajiya ta birnin Shanghai. Domin yadda take da kwarewa kan al'adun kananan kabilu tare da harsunansu, a yanzu haka tana kulawa da dalibai 'yan kananan kabilu a jami'ar.

A watan Satumba na kowace shekara, Hong Hanying ta kan tara dalibai sabbin zuwa na kananan kabilu a wuri daya, don fahimtar abubuwan da suke bukata, tare kuma da ba su taimako, kuma irin kokarin da take yi ya samu amincewa daga daliban. A game da yadda aka zabe ta a matsayin wakiliyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Hong Hanying ta ce,"ina alfahari da yadda aka zabe ni a matsayin wakiliyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, baya ga haka, ina ganin wannan babban nauyi ne da aka dora a kaina."

Su Wei Dengdian da Memetcan Umer da Hong Hanying kadan ne daga cikin 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da suka fito daga kananan kabilu. Wang Jingqing, mataimakin shugaban sashen shirye-shirye na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana cewa,"Daga cikin wakilan da aka zaba, 'yan kananan kabilu na karuwa, wadanda yawansu ya kai 249, adadin da ya karu da kaso 7 sama da na taron wakilan jam'iyya a karo na 17, wato kaso 11 bisa dari na daukacin wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke nan."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China