in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin na kokarin jawo al'umma cikin harkokin diplomasiyya
2012-10-24 18:11:55 cri






Cikin shekaru 10 da suka wuce, manufofin diplomasiyya na kasar Sin da kuma matakan da ta dauka su kan jawo hankalin kasa da kasa. Kasashen duniya na kara bukatar fahimtar manufofin diplomasiyya na kasar Sin, jama'ar kasar ma suna kara himma wajen sa hannunsu cikin harkokin diplomasiyya na kasar. A Sa'i daya, bayan da jam'iyyar kwaminis da ke mulki a kasar Sin ta gabatar da manufar "samun ci gaba ta hanyar kimiyya", gwamnatin kasar Sin ta kara mai da hankali a kan bukatun al'umma wajen gudanar da ayyukan diplomasiyya. Bisa ga wannan ra'ayi na harkokin diplomasiyya domin amfanawa al'umma, kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri wajen jawo al'umma cikin harkokin diplomasiyya.

"kwanan nan, na ji labarin rashin kwanciyar hankali a kasashen da ke makwabtaka da mu, abin da ya haifar da matsala gare mu ta fannin diplomasiyya. A game da lamarin, shin wadanne matakai ne ma'aikatar harkokin waje za ta dauka?"Wannan tambaya ce da wani dattijo dan shekaru 82 a duniya wanda ya fito daga karkara ya yi wa shugaban sashen yada labarai na ma'aikatar harkokin waje a watan Oktoba na shekarar 2009. A waccan rana, dattijon ya shiga dakin watsa labarai da ke ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, domin halartar bikin ranar bude harkokin diplomasiyya ga al'umma da ma'aikatar ta fara gudanarwa tun shekarar 2003, inda ya mika tambayoyinsa ga jami'an diplomasiyya na kasar. Bayan da aka shafe tsawon shekaru kusan 10, bikin ranar bude harkokin diplomasiyya ga al'umma ya zamanto wani dandali ga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin na jawo al'umma cikin tafiyar da harkokin diplomasiyya na kasar.

Ma'anar jawo al'umma cikin tafiyar da harkokin diplomasiyya ita ce bisa ga jagorancin gwamnati, al'umma daga bangarori daban daban sun yi kokarin sa hannunsu a ciki, domin fadakar da al'ummar kasashen ketare a kan halin da kasar ke ciki, tare kuma da fadakar da al'ummar kasar a kan harkokin diplomasiyya da kasar ke gudanarwa. A yayin da kasar Sin ke kara cudanya da kasashen duniya a shekarun baya, jawo al'umma cikin harkokin diplomasiyya ya fara zamantowa wani sabon bangare na ayyukan diplomasiyya da gwamnatin kasar ke gudanarwa. A game da dalilin da ya sa al'umma ke kara shiga cikin harkokin diplomasiyya, Mr.Ma Zhengang, tsohon jakadan kasar Sin a Birtaniya, yana ganin cewa, hakan ya faru ne a sakamakon yadda kasar Sin ke kara samun ci gaba ta fannoni daban daban. Ya ce,"An samu manyan sauye-sauye kan huldar da ke tsakanin Sin da duniya. Da ba a mai da hankali a kan kasar Sin ba, amma yanzu sakamakon yadda ta samu ci gaba da ba da tasirinta a duniya, tana bukatar bin hanyoyi daban daban domin bayyana manufofinta ga kasashen ketare."

Domin kara fahimtar da kasashen duniya a kan kasar Sin, a kan yi amfani da ziyarce-ziyarcen aiki da shugabannin kasar ke gudanarwa wajen jawo al'umma a cikin harkokin diplomasiyya. A watan Faburairu na shekarar 2009, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyara kasar Mauritius, inda bayan ganawa da shugabannin kasar, ya je cibiyar al'adun kasar Sin da ke Port Louis, babban birnin kasar, domin ganawa da al'ummar wurin da ke koyon Sinanci tare da shakatawa da wakokin gargajiya na kasar Sin.

A yanzu haka, shugabanin kasar Sin suna ta kara mu'amala da yin musayar ra'ayi tare al'umma da suka fito daga bangarori daban daban a yayin da suke ziyara a kasashen waje, ta haka, an kusantar da kasar Sin da kasashen duniya, kuma an karfafa fahimtar juna a tsakaninsu.

A waje daya kuma, a yayin wasu muhimman tarurukan duniya, tawagar gwamnatin kasar Sin ta kuma kafa cibiyar labarai, don ganawa da manema labarai, tare da kara fahimtar da al'ummar duniya a kan manufofin diplomasiyya na kasar Sin.

Ban da fadakar da al'ummar kasashen ketare a kan kasar Sin, gwamnatin kasar tana kuma kokarin fadakar da jama'arta a kan harkokin diplomasiyya da take gudanarwa. A farkon wannan shekara, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta hada gwiwa da wasu manyan tashoshin yanar gizo na kasar, wadanda suka shirya wata tattaunawa a tsakanin shugabannin ma'aikatar da kuma masu ziyartar shafukan internet na kasar game da manufofin diplomasiyya na kasar Sin. Ta haka, an kara fahimtar juna a tsakanin gwamnati da al'umma na kasar. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China