in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban taron wakilan JKS na 18 zai daukaka ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka
2012-10-17 16:02:35 cri

Jakadan kasar Nijeriya dake kasar Sin Alhaji Aminu Bashir Wali ya fada a yau Laraba 17 ga wata a nan birnin Beijing cewa, babban taro na karo na 18 na wakilan duk kasa na jam'iyyar kwaminis ta Sin da za a kira zai sa kaimi ga bunkasuwar kasar Sin kuma ga dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

Yayin da ya gana da wakilinmu, Aminu Bashir Wali ya ce, ci gaban da Sinawa suka samu a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin ba ma kawai zai taimakawa jama'arta ba, har ma zai taimakawa nahiyar Afrika wajen raya tattalin arzikinta da kiyaye zaman lafiya da dorewa na duniya.

Ban da wannan kuma, jakada Aminu Bashir Wali ya ce, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin, gwamnatin kasar ta dade tana dukufa kan bunkasa dangantakar hadin kai ta abokantaka da kasashen Afrika, har ma ta ba da sahihin taimako ga kasashen Afrika don warware matsalolin da suka samu bisa hanyarsu ta samun bunkasuwa, wannan na sanin kowa ne, haka ma ta samu amincewa daga jakadun kasashen Afiraka dake kasar Sin. Ya yi imani da cewa, taron zai sa kaimi ga kara bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China