Taron hukumar karkashin jagorancin shugaba Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, ya yi nazarin abubuwan da ake saran gudanarwa a tarukan watan Nuwamba.
Babban taron wani muhimmin ganawa ce ta jam'iyyar da za a gudanar a wani muhimmin lokaci da kasar Sin ke kokarin gina al'umma ta gari daga dukkan fannoni, da gudanar da gyare-gyare a cikin gida tare da bude kofa ga kasashen waje, gudanar da canje-canjen tattalin arziki a fannoni daban-daban.
Babban taron zai kara bayyana tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin, nazarin ayyukan da jam'iyyar ta gudanar cikin shekaru biyar da suka gabata da kuma abubuwan da jam'iyyar ta aiwatar tun babban taron jam'iyyar karo na 16.
Bugu da kari, taron zai yi nazarin darussan da jam'iyyar ta koya a baya daga lokacin da ta yi kokarin hada kan al'ummar kasar ta yadda ake jagorantar dukkan kungiyoyin kabilun kasar tare da ciyar da akidar kwaminisanci gaba.
Babban taron har ila, zai shata wasu manufofi da dakoki da za su dace da zamani tare da biyan bukatun al'umma.
A cewar taron, za kuma a zabi sabbin mambobin kwamitin tsakiya na JKS da sabuwar hukumar ladabtarwa. (Ibrahim)