in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta samar da irin masara mai inganci guda 2 da za su samar da sinadarin Vitamin-A
2012-07-25 11:40:48 cri
Cibiyar kasa da kasa da ke nazarin aikin gona a yankuna masu zafi (IITA) ta fada a ranar Talata cewa, kasar Najeriya ta samar da sabbin irin shuka na masara guda 2 wadanda za su iya samar da karin sinadarin Vitamin-A a cikin abincin miliyoyin jama'a a kasar.

Wata sanarwar da cibiyar ta bayar, wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu, ta bayyana cewa, kwamitin tantance irin shuka na Najeriya ne ya bayyana nau'in farko na irin masara mai ingancin da ke kunshe da sinadarin Vitamin-A a ranar 4 ga watan Yulin shekara ta 2012, a matsayin Ife maizehyb 3 da kuma Ife maizehyb 4. An dauki wannan mataki ne da nufin magance matsalar karancin sinadarin Vitamin-A da ake fuskanta.

Sanarwar ta ce, cibiyar ta IITA tare da hadin gwiwar cibiyar nazari da samar da horo kan aikin gona (IAR&T) ne suka bunkasa irin masaran da ke kunshe da sinadarin na Vitamin-A.

Sauran cibiyoyin da ke cikin wannan hadin gwiwa a cewar sanarwar, sun hada da cibiyar binciken aikin gona da ke Zaria (IAR), jami'ar Maiduguri, cibiyar noman masara da alkama ta kasa da kasa (CIMMYT), jami'ar Illinois da jami'ar Wisconsin dukkansu a kasar Amurka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China