A lokacin hirar su Mukadashin jakadan kasar Sin da ke Nijeriya Mista He Meng, ya ce dandalin tattauna kan hadin kai da ke tsakanin Sin da Afirka ya sa kaimi sosai ga dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.
Mista He ya ce, ya shafe shekaru 8 yana aiki a kasashen Afirka, kuma sau uku yana shiga cikin aikin share fage na dandalin tattaunawa kan hadin kai da ke tsakanin Sin da Afirka, wanda ya ba shi damar fahimtar dandalin tattaunawar da kuma muhimmancin da yake da shi matuka ga bangarorin biyu na Sin da Afirka, wanda ta wannan hanya bangarorin biyu suka samu nasarori masu yawa a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da cinikayya da al'adu da dai sauransu.
Mista He ya yi bayanin cewa, taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka zai gudana a ranar 19 zuwa 20 ga watan da muke ciki. Ya yi imanin cewa, bangarorin biyu za su dauki sababbin matakai domin kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakarsu. (Danladi)