in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suke yin amfani da wayoyin salula ya zarce biliyan 1.03 a kasar Sin
2012-05-24 16:43:59 cri
Bisa kididdigar da ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da sadarwa ta Sin ta bayar a ran 23 ga wata, an ce, daga watan Janairu zuwa watan Afrilu na bana, yawan mutanen da suke yin amfani da wayoyin salula ya karu da miliyan 43.799, wato ke nan daukacin yawan masu amfani da wayoyin salula ya kai biliyan 1.03 a kasar Sin, cikinsu an kara samun mutanen da suka yi amfani da wayoyin salula ta fasahar zamani ta 3G da yawansu ya kai miliyan 30.547, kuma daukacin mutane masu yin amfani da wayoyin salula ta fasahar 3G ya kai kimanin miliyan 158.971.

Haka kuma, daga watan Janairu zuwa watan Afrilu, an kara samun gidajen da suke amfani da yanar gizo ta Internet da ya kai miliyan 9.306, wato ke nan dukkan gidajen da suke amfani da yanar gizo ya kai miliyan 159.307.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China