Bikin nuna majigin zai taimakawa mutanen kasar gane wa idanunsu sha'anin silima a kasar Gabon da ya kwashe tsawon shekaru hamsin, ta yadda za su fahimci wasu muhimman matakai, zamani da lokaci kamar yadda jami'an suka bayyana.
Haka kuma zai taimaka wajen kafa wata al'adar harkokin silima ta kasa. A tsawon kwana bakwai, mutanen kasar zasu yi kallon fina finan da kasar ta tsara. Sannan za'a maida hankali bisa nuna fina finai iri daban daban. Kuma bikin ya kasance wata babbar gada tsakanin lokacin da ya wuce, zamani yanzu da zamani mai zuwa.
Fim din farko na kasar Gabon na da tsawon lokaci na mintoci 20, kana an shirya shi a shekarar 1971, fim din na magana kan zulumin zaman al'umma a idon wani mai shirya fim da ya dawo kasarsa bayan samun 'yancin kan kasashen Afrika. (Maman Ada)




