A 'yan kwanakin nan, wasu kasashen yamma suna kara kakabawa kasar Iran takunkumi, lamarin da ya tsananta halin da ake ciki a yankin Gulf. Mista Liu ya ce, kasar Sin tana ganin cewa hakan ba zai amfana wajen daidaita matsalar Iran ba, kuma tana nuna damuwa kan wannan batu.
Mista Liu ya kara da cewa, kasar Sin ta bada shawarar daidaita sabani da rikici tsakanin kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari, kuma sanya takunkumi da kara matsa lamba har ma da yin barazana da karfin soji, sam ba za su taimaka wajen warware matsala ba, sai ma su tsananta halin da ake ciki.(Murtala)