in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Habasha za ta karbi bakuncin babban taron duniya kan lafiyar jama'a karo na 13 da za a yi a shekarar 2012
2011-12-06 11:47:31 cri
A ranar 5 ga watan Disamba kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito cewa, kasar Habasha za ta karbi bakuncin babban taron duniya karo na 13 da za a yi kan sha'anin lafiyar jama'a a shekarar 2012, kamar yadda kungiyar lafiyar jama'a ta kasar Habasha mai zamana kanta(EPHA) ta sanar.

Babban taron da ake shiryawa karkashin hadin gwiwa tsakanin kungiyar EPHA mai zaman kanta da hukumar lafiya ta duniya za a yi shi ne a babban dakin taron MDD da ke Addis Ababa, wanda zai samu kulawa karkashin jagorancin ministan lafiya na kasar Habasha Tewodoros Adhanon.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Litinin din da ta gabata, Mr Solomon Abebe, jami'in tsare-tsare kan harkar sadarwa na kungiyar EPHA, ya ce za a fara gudanar da babban taron tun daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Afrilun shekara mai kamawa, wanda ake maiyar da ''dama da barazanar dake tattare da harkokin lafiya a duniya" a matsayin babban takensa.

Mr Solomon ya kara da cewa, ana sa ran ganin babban taron zai ja hankalin mutane a kalla 3000, wadanda ke hada da masu bincike kan lafiyar jama'a, malaman jami'o'i, masana kimiyya, masu fadakarwa, masu shirye-shirye, masu tsara doka da dalibai na duk duniya.

A cewar kungiyar ta EPHA, babban taron na matsayin wata babbar kungiya da za ta bada dama wajen musayar ilmi da gogewa kan lafiyar jama'a tare da bada gudummowa wajen kariya da cigaban lafiyar jama'a a matakin duniya, nahiya da kasa.(SALAMATU)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China