Wasu gajerun fina finai fiye da goma sha biyar da suka fito daga kasashe 15 ne aka shigar dasu cikin wannan bikin nuna fim da za'a gabatarwa jama'a a cikin dakunan nuna fim dake birnin.
Yin hakan na daga cikin manufar masu shirya bikin na maido da martabar harkokin silima na kasar Gabon musammun ma na baiwa matasan kasar dake da fasaha kan wannan sana'a dama don su nuna kwarewarsu a cikin harkokin da suka shafi tsara fim da shirya shi.
Haka kuma manufar wannan biki itace ta janyo hankalin mutanen kasar Gabon kan wannan sana'a da ba'a sani ba sosai a cikin kasar, tare da baiwa mutane damar tsara fim na tsawon mintoci 30 domin kara janyo hankalin 'yan kallo kusa da wannan sana'a.(Maman Ada)




