A cikin wadannan tsare-tsaren ayyuka, akwai maganar kafa wata kafar jarida da kuma shagunan saida kayan jiki.
Dukkanin wadannan ayyuka za a mika su cikin hannun nakasassun, ta yadda za su daukar nauyin kansu da kansu.
Tuni aka kafa wani kwamitin da zai rika sa ido kan wadannan ayyuka a karkashin jagorancin wasu hukumomin dake kula da harkokin jama'a bayan sun samu wani horon kara wa juna sani.
Kusan ayyukan da suka shafi sana'ar hannu 150 da mutanen dake tare da wata nakasa suke gudanarwa ne suka samu shiga.
Haka kuma gwamnatin kasar tana shirin bunkasa taimakon da take baiwa nakasassun kasar a nan gaba.(Maman Ada)




