in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya
2011-05-18 15:20:54 cri
Ibrahim: A yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wato hukumar koli mai kula da harkoin kafa dokoki ta kasar inda a watan Maris, aka zartas da wata takardar dake da nasaba da makomar kasar Sin cikin shekaru 5 masu zuwa. Wannan ita ce takardar dake bayani game da "babban shirin na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin na 12", inda aka nuna cewa, kasar Sin za ta fi mai da hankali kan yadda za a iya samun makamashi maras gurbata muhalli, kamar su makamashin iska da na hasken rana da dai makamatansu. Sannan, ta tsara wasu burin da take son cimmawa domin kokarin rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya.

Sanusi: Mr. Zhang Ping, shugaban kwamitin neman ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta tsara burin da take son cimmawa cikin shekaru 5 masu zuwa ta fuskar tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya. Mr. Zhang ya bayyana cewa, "Ya kasance burin da tilas za a cimma, mun tabbatar da cewa, ya zuwa shekarar 2015, yawan makamashin da ake amfani da shi ya ragu da kashi 16 cikin dari bisa a shekarar 2010, kana yawan abubuwa masu dumama yanayin duniya da ake fitarwa zai ragu da kashi 17 cikin dari, sannan yawan abubuwa masu gurbata muhalli da za a fitar da su ya ragu daga kashi 8 zuwa kashi 10 cikin kashi dari."

Ibrahim: Malam Sanusi, yau shekaru 5 ke nan da suka gabata, kuma shi ne karo na farko da gwamnatin kasar Sin ta kafa wani burin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli a cikin shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin na 11, inda ta nemi a rage yawan makamashin da ake amfani da shi kusan kashi 20 cikin kashi dari, kana yawan abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa ya ragu da kashi 10 cikin kashi dari. Wannan ya kasance wani burin da ya zama tilas da ta yi kokarin cimmawa a cikin shekaru 5 da suka gabata. Saboda haka, gwamnatoci a matakai daban daban na kasar Sin da masana'antu sun yi kokari a fannoni da yawa domin kokarin cimma wannan buri. A sanadiyyar kokarinsu, yawan makamashin da aka yi tsimi a kasar Sin ya kai kamar kwal ton miliyan dari 6, kuma yawan abubuwa masu dumama yanayin duniya da ba a fitar da su ba ya zarce ton miliyan 6.

Sanusi: Amma kuma malam Ibrahim, gwamnatoci a matakai daban daban na kasar Sin ba su ji dadin sakamakon da suka samu ba, bisa sabon shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, an fitar da sabon burin yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da ake son cimmawa.

Ibrahim: Malam Sanusi, yana da kyau masu sauraro su fahimci cewa, makamashi mafi muhimmanci da kasar Sin take dogara kansa shi ne kwal Bisa dokokin dake kunshe cikin "takardar bunkasa birane wadanda suke fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya kalilan" da cibiyar nazarin ilmin zaman al'ummar kasar Sin ta fitar kwanan baya, ba abin da ya canja a halin da ake ciki. Amma yanzu kasar Sin na kokarin canja irin wannan yanayi. Sakamakon haka, tabbas ne kasar Sin za ta kara fuskantar kalubaloli ta fuskokin kudi da fasaha.

Sanusi: E, haka ne. Malam Ibrahim, lardin Shanxi, da ya kasance tamkar sansani mafi muhimmanci a kasar Sin wajen samar da makamashin kwal wuri ne mai gurbata muhalli mafi tsanani a kasar Sin a da. Yanzu gwamnatin lardin Shanxi tana tsara manufofin yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli bisa shirin na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin. Mr. He Zhongwei, wani jami'in dake aiki a hukumar kiyaye ingancin muhalli ta lardin Shanxi ya gaya wa wakilinmu cewa, "Za a rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli da wasu manya masana'antu suke fitarwa, kuma za a daidaita nau'o'in kayayyakin da suke samarwa domin canja tsohon salon neman ci gaba, da kuma yin kokarin neman ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba. Sannan za mu kara karfin daidaita tsarin masana'antu, wato za mu daina yin amfani da wasu nau'rorin da suka tsufa, har ma za mu rufe wasu masana'antu wadanda ba sa dacewa da zamani, kuma suke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli sosai."

Ibrahim: Aikin rage fitar da abubuwa masu dumama yanayin duniya ya kasance wani muhimmin aiki ga masana'antun da ake sarrafa bakin karfe wadanda suke bukatar makamashi da yawa, kuma suke fitar da abubuwan dake gurbata muhalli sosai. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan makamashin da ake amfani da shi a masana'antun zamani ya kai kimanin kashi 70 cikin kashi dari bisa jimillar makamashin da ake amfani da shi a duk kasar, kana yawan makamashin da ake amfani a masana'antun da ake sarrafa bakin karfe ya kai kashi 15 cikin dari daga cikinsu. A cikin shekaru 2 da suka gabata, masana'antun da ake sarrafa bakin karfe na kasar Sin sun shiga uku, wato suna fuskantar hauhawar farashin tama da karafe da gurbataccen yanayi, yanzu suna fuskantar wata sabuwar jarrabawa.

Sanusi: Kamfanin sarrafa bakin karfe na Taiyuan wanda yake birnin Taiyuan, hedkwatar lardin Shanxi, na daya daga cikin irin wadannan kamfanoni mafi girma a duniya. Yanzu shi ma dole ne ya mai da hankali kan yadda zai iya yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli domin neman kasancewa tare da birnin. A cikin shekaru 5 da suka gabata, wannan kamfanin da ya taba fitar da dimbin abubuwa masu gurbata muhalli ya zuba kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 8 kan na'urorin yin tsimin makamashi da na'urorin da suke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, kuma yana kokarin bunkasa tattalin arzikin bola jari. Mr. Han Sen wanda yake aiki a wannan kamfani ya ce, bisa kokarin da kamfanin ya yi cikin shekaru 5 da suka gabata, ya ci moriya sosai ta fuskokin tattalin arziki da zaman al'umma. Yanayi na birnin Taiyuan ma ya samu ingantuwa. Kamar yadda Mr. Han Sen ya ce, "A cikin shekaru 2 da suka gabata, kamfanin sarrafa bakin karfe na Taiyuan na mai da hankali wajen sake yin amfani da zafi domin samar da wutar da yawanta ya kai kilowatts miliyan 1200 a kowace shekara. Amma a da, ba mu yi amfani da irin wannan karfin wuta ba. Sakamakon haka, muka yi tsimin makamashin kwal da yawansa ya kai kimanin ton dubu dari 5, kuma yawan abubuwa masu dumama yanayin duniya da ba su fitar da su zuwa sararin sama ba ya kai kimanin ton miliyan 1 da dubu 100."

Ibrahim: An labarta cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa, wato lokacin da kasar Sin take aiwatar da sabon shiri na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin, kamfanin mulmula bakin karfe na Taiyuan zai ci gaba da aiwatar da wasu ayyukan yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli domin hanzarta kafa tsarin raya tattalin arziki na bola jari.

Sanusi: malam Ibrahim, yanzu, bari mu yi tattaki zuwa wani birni daban, wato birnin Wuxi dake gabashin kasar Sin. Birnin Wuxi, birni ne da ba shi da isashen makamashin da ake bukata, kuma yana kasancewa a bakin tafkin Taihu. Sabo da haka, ba a iya gurbata shi sosai ba. Amma yaya wannan birni yake samun ci gaba? Mr. Mao Xiaoping, magajin birnin Wuxi ya ce, a lokacin da ake aiwatar da "shiri na shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin na 12", birnin Wuxi zai kara mai da hankali wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani, da kuma daidaita tsarin tattalin arzikinsa. Mr. Mao ya ce, "Da farko dai, za mu hanzarta daidaita tsarin tattalin arziki, da bunkasa masana'antun fasahohin zamani. Sannan za mu hanzarta bunkasa sana'o'in ba da hidima, kamar su sana'ar manhaja da al'adu da dai makamatansu. Bugu da kari, za mu kara yin kokarin bunkasa sabbin masana'antu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China