in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasuwa na kasar Sin sun samu kasuwa lokacin da ake share fagen bikin auren yarima William na Ingila
2011-04-18 09:17:57 cri
Garba: A ran 29 ga watan nan na Afrilu, za a shirya wa yarima William na kasar Ingila da budurwarsa Kate Middleton bikin aure da 'yan kasar suka yi ta jira har tsawon shekaru 30. Sabo da haka, wannan bikin aure yana jawo hankalin jama'a sosai a duk fadin duniya. Kamar yadda duk wadanda suke shirya bikin aure suke yi, yanzu masarautar kasar Ingila tana shan aikin share fagen wannan bikin aure. An kiyasta cewa, yawan kudin cinikayya, kamar kayayyakin tunawa da yawon bude ido da suke da nasaba da wannan bikin aure zai kai fan biliyan 1. Saboda haka, ko shakka babu, 'yan kasuwa na kasar Sin wadanda suka shahara sosai wajen kere-kere ba za su kyale wannan damar samun kudi ba. Alal misali, faya-faye da zobban aure da suke da nasaba da bikin aure na yarima William, dukkansu kayayyakin tunawa ne da aka kera a kasar Sin.

Sanusi: A cikin sa'o'i 8 kawai bayan da masarautar Ingila ta bayyana hoton aure na yarima William da Kate Middleton, wani kamfanin sayar da kayayyakin tunawa dake garin Yiwu na kasar Sin ya soma sayar da sabbin zobban lu'ulu'u da suka yi kama da surar zoben lu'ulu'u na marigayiya Diana Spencer, wato mahaifiyar William a shafuffukansu na intanet, inda masu karanta shafin intanet suka yi ta hanzarin sayensu. Mr. Zhou Mingwang, babban direktan wannan kamfanin cinikin kayayyakin ado ya ce, "Ya kasance tamkar wani kamfanin samar da kayayyakin ado, muna mai da hankali sosai kan nau'o'in kayayyakin ado da suke karbuwa a gida da ma kasashen waje, musamman muna kokarin sanya abubuwan da suke wakiltar al'adun kasashen Turai a cikin kayayyakinmu."

Garba: Mr. Zhou Mingwang ya ce, 'yan kasuwa na garin Yiwu suna mai da hankali sosai kan yadda za a samu damar yin kasuwanci a lokacin da ake murnar muhimman shagulgula da gasanni iri iri. Su kan soma samar da kayayyakin ado musamman ga muhimman shagulgula da gasanni iri iri. 'Yan kasuwa na kasar Ingila sun sani, cewar kananan kayayyakin ado da a kan kera da kuma sayar a garin Yiwu suna da arha sosai. Saboda haka, su kan je garin Yiwu domin sayen kayayyakin da suke bukata kai tsaye. Mr. Zhou ya yi hasashen cewa, za a iya hanzarta sayen wadannan zobban lu'ulu'u har zuwa lokacin kammala bikin auren yarima William. Ko shakka babu, lokacin da 'yan kasuwa na garin Yiwu suke kera wannan zobe, sun yi dan gyara kan sura domin magance matsalar satar ikon mallakar fasaha.

Sanusi: A hakika dai, aikin da ya zama dole ne 'yan kasuwa na garin Yiwu su yi a kowace rana shi ne karanta labaru a shafin yanar gizo a kokarin neman damar samun kasuwa. A lokacin da aka shirya bikin Expo na Shanghai a kasar Sin da gasar wasan kwallon kafa ta FIFA a kasar Afirka ta kudu a bara, 'yan kasuwa na garin Yiwu sun samu riba da yawa wajen sayar da kananan tutocin kasashen duniya da kakaki Vuvuzela da rigunan kungiyoyin kwallon kafa da dai makamatansu.

Garba: Bayan da suka samu wannan moriya, yanzu kamfanonin dake garin Yiwu suna kokarin samun riba a albarkacin wannan bikin auren yarima William. Ba ma kawai suna sayar da zobban lu'ulu'u ba, har ma sun bubbuga hotunan yarima William da budurwarsa Kate Middleton a kan kofuna, rigar T-shirt da zobban mabudi. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, goman kamfanonin samar da kayayyaki irin wadannan ne ke da nasaba da wannan bikin aure.

Sanusi: Yanzu mai da hankali kan labaru da dumi-dumi da suke faruwa a duk fadin duniya domin samun kasuwa ya zama muhimmiyar hanyar neman kudi da kamfanoni manya ko kanana na garin Yiwu suke bi. Yanzu kamfanonin kera da kuma sayar da kayayyakin ado ba safai su kan samu riba da yawa ba. Mr. Chen Jiru, babban sakataren kungiyar masana'antun samar da kayayyakin ado ta lardin Zhejiang ya bayyana cewa, "Yanzu yawan ribar da kamfanonin samar da kayayyakin ado na Yiwu suke samu dan kadan ne. Sakamakon haka, kamfanoni da yawa na garin Yiwu suna kokarin kirkiro sabbin fasahohi da hanyoyi na kera da kuma sayar da kayayyakin ado a kokarin samun karin riba."

Garba: Malam Sanusi, 'yan kasuwa na garin Yiwu suna kokarin neman damar yin kasuwanci bisa al'amura dake da dumi dumi, amma akwai wani kamfanin kera kayayyakin fadi-ka-mutu na birnin Tangshan dake kusa da birnin Beijing ya samu wata kwangilar samar da kayayyakin fadi-ka-mutu dubu 45 ga bikin aure na William daga masarautar Ingila. Wannan wani albishiri ne ga kamfanin. Kuma an riga an yi sufurin wadannan kayayyakin fadi-ka-mutu zuwa kasar Ingila a watan Janairu na bana. A kan wadannan kayayyakin fadi-ka-mutu, an mammanna hotunan yarima William da budurwarsa Kate Middleton.

Sanusi: Ba ma kawai wannan kamfanin kasar Sin ya samu kwangila daga masarautar Ingila ba, a bara, lokacin da gimbiyar masarautar Sweden take neman kayayyakin tunawa domin bukin aurenta, ta samu irin wannan kayan fadi-ka-mutu, tana so sosai, sabo da haka, ta yi oda don sayensu. Game da wannan albishiri, madam Li Sufen, wadda ke tafiyar da wannan kamfani ta ce, masarautar Sweden tana jin dadin inganci da fasahohin kera irin wannan kayan fadi-ka-mutu, ba ta taba tura ko mutum guda da ya zo kasar Sin domin binciken ingancin kayansu ba ko sau daya, kuma ba a samu aibu ko guda ba a kan wadannan kayayyakin da yawansu ya kai dubu 50, kuma darajarsu ta kai kimanin dala dubu 150. Madam Li Sufen ta ce, "A bara, na bai wa gimbiyar kasar Sweden Victoria wani faranti mai girman inch 20, inda muka manna hoto na ita da saurayinta. Daga baya, na ji an ce, a gun bikin aure, abin kyauta da gimbiyar ta fi so shi ne wannan farantin da muka ba ta, kuma ta sanya shi a wani wurin da ya fi muhimmanci a dakinsu."

Garba: Yauwa, na gane, masarautar Ingila ta san wannan kamfanin kasar Sin dake birnin Tangshan ne a yayin bikin aure na gimbiyar kasar Sweden. Sannan ta tuntubi kamfanin din da kuma bai wa wannan kamfanin kwangilar sayen kayayyakin fadi-ka-mutu. Darajar wannan kwangila ta kai fiye da dala dubu dari 3.

Sanusi: A ganin madam Li Sufen, yawan kudin cinikayya da kamfaninta ya samu daga masarautun Ingila da Sweden kalilan ne, wato bai wuce kimanin kashi 5 cikin dari kawai ba bisa jimillar kudin cinikayyar da kamfanin ya samu a bara, amma ba za a iya kiyasta kyakkyawan tasirin da wadannan kwangiloli biyu suka kawo wa kamfanin ba. A lokacin da aka shirya bikin aure na gimbiyar Sweden, gidan talibijin na kasar Sweden ya tsara da kuma yada wani shirin musamman game da masana'antun samar da kayayyakin fadi-ka-mutu na birnin Tangshan. Madam Li ta ce, wannan talla kyauta ce.

Garba: Malam Sanusi, a ganina, ko 'yan kasuwa na garin Yiwu sun iya sayar da kananan kayayyakinsu a duk sassan duniya, ko kamfanonin samar da kayayyakin fadi-ka-mutu sun fitar da kayansu zuwa masarautun kasashen Turai, muhimmin dalilin da ya sa suka iya samun nasara shi ne 'yan kasuwa na kasar Sin sun kware sosai wajen neman samun damar yin kasuwanci, kuma suna da wani tsarin samar da kayayyakin da ake bukata cikin hanzari, kana kayayyakinsu suna da inganci. Yanzu 'yan kasuwa na kasar Sin suna kokarin samun kasuwa a duk duniya lokacin da ake kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya don zama na bai daya, kuma sun samu riba kwarai. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China