in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An riga an kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS
2011-03-31 15:05:52 cri
Jama'a masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Da fatan kome na gudana kamar yadda ake bukata.

A kwanan baya, malam Abdullahi Fazza a Nijeriya ya bugo mana waya cewa, "Na ji an ce za a kaddamar da taron koli na kasashen BRICS, ko ba haka ba? Don Allah ku ba ni wani bayani kan wannan tsari na hadin gwiwa na kasashen BRICS."

To, malam Abdullahi Fazza, kamar yadda ka bayyana, a tsakiyar watan Afrilu, za a kira taron koli na kasashen BRICS a lardin Hainan na kasar Sin. Kafin wannan a ran 24 ga watan Maris, wasu masana daga kasashen BRICS sun bayyana cewa, an riga an kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS. Hakan ya kara karfin wadannan kasashe masu karfin tattalin arziki na fada a ji a yayin da suke magana da kasashen yammacin duniya. Duk da haka kuma, ba su dauki niyyar yin takara da kasashe masu sukuni ba.

A wannan rana, mataimakin shugaban kwalejin nazari kan dangantaka tsakanin kasa da kasa na jami'ar Beijing, Guan Guihai ya bayyana cewa, an riga an kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS ta hanyar daukar matakin ganawa tsakanin shugabannin wadannan kasashe a matsayin babban tushen tabbatar da wannan hadin gwiwa da dai sauransu.

A shekarar 2001, Jim O'Neill, babban masani kan tattalin arziki dake aiki a kamfanin Goldmansachs na Amurka ya fara tunanin wannan ra'ayi na "Kasashen BRICS" a karo na farko a duniya, wadanda suka hada da kasashen Brazil, Rasha, Indiya, da kuma Sin. A watan Yuni na shekarar 2009, shugabannin kasashen BRICS sun yi ganawar farko a hukunce a kasar Rasha. Sai daga bisani, a watan Disamba na shekarar 2010, kasashen BRICS sun cimma matsaya daya wajen shigar kasar Afirka ta Kudu cikinsu.

Guan Haigui ya bayyana cewa, yanzu kasashen BRICS ba su kasance tamkar wata kungiya ba, ko wani tsarin yin shawarwari. Suna hada gwiwa a fannonin masana'antu, cinikayya, kiyaye muhalli da dai sauransu tare ta yadda za su samun sakamako mai kyau. Idan ana iya yin hangen nesa, za a tarar da cewa, wannan tsarin hadin gwiwa yana da karfi sosai wajen samun bunkasuwa da samar da sabbin kayayyaki.

Shugaban cibiyar nazari kan harkokin duniya ta Shanghai, Yang Jiemian ya nuna cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS wani muhimmin kashi ne dake cikin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, kuma ya kara karfin kasashe masu karfin tattalin arziki na fada a ji a yayin da suke magana da kasashe masu sukuni, har ma ya kiyaye babbar moriyar kasashe masu tasowa baki daya.

Wani ma'aikacin cibiyar nazari kan maganganu tsakanin kasa da kasa ta Afirka ta Kudu ya furta cewa, kasashen BRICS suna kara karfinsu a yau da kullum a dandalin siyasa na duniya. Sun shiga muhimman harkokin duniya. A sabili da haka, suna taka rawar a zo a gani a dandalin duniya.

Ban da haka, wasu sauran masana sun bayyana cewa, a gun taron ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS a karo na uku da za a yi a birnin Sanya na Sin, ana sa ran kara samun ci gaba a wannan fanni bayan da aka waiwayo hadin gwiwa da aka yi a tsakaninsu a baya.

Shugaban hukumar nazari kan gabashin Asiya ta cibiyar kimiyya da fasaha ta Rasha ya bayyana cewa, "A bakin Sinawa, bulo na zinariya, wato BRICS, ba na nufin wani irin kayan ado ba. Wannan ya bayyana fatanmu, wato muna sa ran cewa, hadin gwiwa tsakaninmu zai kara samun daraja, kamar zinariya. Kuma za a iya yin amfani da shi, daidai kamar yadda bulo yake.

Jama'a masu karanta, bayani ke nan kan tambayar malam Abdullahi Fazza a Nijeriya, da fatan ka ji ka gamsu da wannan bayani. Kuma za a kaddamar da taron koli na kasashen BRICS a tsawon wasu kwanaki kawai. Ko kuna sha'awar sanin abubuwan da za a tattauna kansu, ko sakamako da za a samu a wannan taro? Ko zai yi tasiri ga kasashen Afirka a nan gaba? To sai ku aiko mana da wasiku domin bayyana ra'ayoyinku, mun gode.

Bayan haka, a makon jiya, mun samu sakwanni da dama daga masu sauraronmu. A cikinsu, akwai malam Abdoulaye Djibrila a Nijeriya da ya rubuto mana cewa, "Har yanzu ba ku kiran sunana kamar yadda ya dace ba. Cikekken sunana shi ne Abdoulaye Djibrila. Ina fatan kun fahimce ni a wannan karo."

To, malam Abdoulaye Djibrila, don Allah ka gafarce mu. Lallai wannan kuskure namu ne. Amma mun yi alkawarin cewa, ba za mu sake yin irin wannan kuskure ba a nan gaba. Da fatan za ka ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryenmu. Mun gode.

Bayan haka, a gami da ziyarar mataimakin firaministan kasar Sin Wang Qishan a kasashen Afirka bisa goron gayyata, mai sauraronmu a kullum malam Salisu Muhammad Dawanau a Nijeriya ya aiko da sakon cewa, "Hakika wannan ziyara tana da kyau, musamman sabo da yanayin da kasashen Afirka suke ciki a yanzu. Kasashenmu na Afirka na bukatar samun jagoranci na zumunci da abota ta gaskiya, kuma mai dorewa. Sabo da haka, ina ganin wannan ziyara ta mista Wang Qishan za ta haifar da yawan zumunci da karin moriyar juna a fannoni masu yawa. Na amince da wannan ziyara. Na san sauran mutanen Afirka ma za su amince da ziyarar, musamman ma al'ummar kasashen da ya kai musu ziyara."

To, mun gode, malam Salisu Dawanau. Kasar Sin ta jima tana sada zumunci tare da kasashen Afirka cikin dogon lokaci. A wannan karo, mataimakin firaministan kasar Sin Wang Qishan ya kai ziyara a kasashen Kenya, Zimbabwe, da kuma Angola bisa goron gayyata, tare da isar da gaisuwa da fatan alheri daga dukkan jama'ar kasar Sin ga aminanmu na Afirka.. Muna fatan bisa wannan ziyara, za a kara hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin masana'antu, cinikayya, tarbiyya, kimiyya da fasaha da dai sauransu. Da fatan za mu kara sada zumunci kuma a tsakaninmu, tare da samun ci gaba tare da juna cikin sauri. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China