in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sana'ar cartoon ta samu bunkasuwa a lardin Guangdong
2010-11-30 09:48:57 cri
Ibrahim: Jama'a masu karatu, an samar da daya daga cikin kayan wasan 'yar tsana na Barbie guda 3, wato kayan wasan yara da ake sayarwa kusan a duk fadin duniya a birnin Dongguan na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin. Sauran kayayyakin wasan yara, kamar su Snoopy da Doraemon da Michey da suka shahara sosai a tsakanin yara, an kera galibinsu a birnin Dongguan ne. Yanzu sana'ar yin zane-zanen ban dariya na yara, wato cartoon ta bullo a birnin, kuma ana kokarin kafa sabbin tamburan kayayyakin zane-zanen cartoon a wannan birni.

Sanusi: E, ana iya ganin irin wannan alama a gun bikin baje koli na kare ikon mallakar fasahar yin zane-zanen ban dariya na yara da yin cinikinsu na kasa da kasa karo na biyu da aka shirya a birnin Dongguan. Kamfanoni 506 sun halarci wannan bikin da fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 40, kuma an shafe kwanaki 6 ana yinsa a birnin, inda aka jawo mahalarta dubu dari 6. Wani mutumin da ya kalli wannan biki yana mai cewa, "Yawan ire-iren kayayyakin cartoon da ake nunawa a gun wannan biki ya fi na bara yawa. Kuma galibinsu sabbin zane-zane na cartoon ne na yara."

Ibrahim: An kulla kwangiloli fiye da dubu 1 da darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 12.7 a gun bikin sabo da yadda kayayyakin wasa na cartoon suka samu karbuwa. Wadanda suke tafiyar da wannan sana'a sun bayyana cewa, wani dalilin da ya sa sana'ar tsara zane-zanen ban dariya na yara ta samu ci gaba cikin sauri a birnin Dongguan shi ne ana mai da hankali sosai kan kare ikon mallakar fasaharsu. Mr. Tu Yongqiang, wanda ke tafiyar da wani kamfanin samar da kayayyakin zane-zane na cartoon ya nuna cewa, "Irin wannan manufa tana da kyau sosai. Abin da ya fi muhimmanci ga sana'ar zane-zanen ban dariya na yara shi ne kare ikon mallakar fasahar tambarin irin wadannan kayayyakin cartoon."

Sanusi: Lardin Guangdong muhimmin lardi ne dake samar da kayayyakin cartoon a nan kasar Sin. Yawan fina-finan cartoon da aka samar a lardin ya kai 40 da tsawonsu ya kai mintoci dubu 21 a cikin watanni 9 da suka gabata, wato yana kan gaba a duk kasar Sin. Mr. Liu Xiaojun, babban direktan kamfanin samar da kayayyakin cartoon na lardin Hunan yana mai cewa, kamfanonin samar da kayayyakin cartoon na birnin Dongguan suna da karfin yin takara a kasuwa, kuma sun fi mai da hankali kan kare tamburansu. Mr. Liu ya bayyana cewa, "Kamfanonin samar da kayayyakin cartoon suna da yawa a birnin. Galibinsu suna son hada kai da juna domin samar da kayayyakin cartoon masu inganci."

Ibrahim: Mr. Yan Xiaohong, mataimakin shugaban hukumar kare ikon mallakar fasaha ta kasar Sin ya amince da irin wannan hanyar da ake bi. A cewar Yan, "Irin wannan hanya tana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban sana'ar samar da kayayyakin cartoon da kuma kyautata tsarin wannan sana'a."

Sanusi: A kan ga kamfanonin samar da kayayyakin cartoon na birnin Dongguan suna cinikin ikon mallakar fasaha. Gwamnatin wurin ta yi kokarin samar da kyawawan manufofi domin sa kaimi ga kamfanonin samar da kayayyakin cartoon da su yi nazari da kuma samar da sabbin kayayyakin cartoon, har ma su yi hadin gwiwa a tsakaninsu domin taimakawa juna. Alal misali, yanzu kamfanonin samar da kayayyakin cartoon su kan hada kan kamfanonin samar da kayayyakin wasan yara domin samar da kayayyakin wasan yara dake da alamun cartoon. Mr. Tang Zeming, wanda ke nazarin zane-zanen cartoon ya bayyana cewa, "Birnin Dongguan tana da kyakkyawar makomar bunkasa sana'ar yin kayayyakin zene-zanen ban dariya na yara. Sabo da haka, mun kafa cibiyar nazarin kayayyakin zane-zanen ban dariya na yara a birnin. Muna fatan za mu iya yin hadin gwiwa da kamfanonin samar da kayayyakin wasa na yara."

Ibrahim: A ganin Mr. Guo Youwei, babban sakataren kwamitin masana'antar da abubuwan al'adu na lardin Guangdong, lardin Guangdong yana da kyawawan sharuda ta fuskar kasuwanci da ba a iya samunsu a sauran wuraren kasar Sin wajen bunkasa sana'ar cartoon.

"Wasu tsoffin kamfanoni suna da kasuwa, sannan sun sake nazarin fasahohin yin kayayyakin cartoon, da kuma sayar da su a kasuwa. Alal misali, kamfanin samar da kayayyakin cartoon na Ao Fei yana kera kayayyakin yara ne kawai, amma yanzu yana nazarin zane-zanen ban dariya na yara, da kuma yin amfani da su kan kayayyakin yara. Sabo da haka, kayayyakinsa suna da kasuwa kwarai." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China