in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dora muhimmanci kan manyan fannoni 4 game da bunkasuwar tattalin arzikin duniya a gun taron koli na birnin Seoul na kungiyar G20
2010-11-11 15:26:34 cri
Za a gudanar da taron koli na kungiyar G20 a karo na 5 a birnin Seoul dake kasar Koriya ta kudu daga ranar 11 zuwa 12 ga wata, inda shugabannin muhimman kasashe 20 na duniya za su tattaunawa kan manyan fannoni 4, wato darajar kudin musaya, da tsarin tabbatar da tsaron hada-hadar kudi na duniya, da yin kwaskwarima kan hukumomin kudi na duniya, da kuma bunkasuwarsu don kyautata manufofin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare, ta yadda za a sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya da kuma warware matsalar hada-hadar kudi ta duniya.

A halin yanzu, tattalin arzikin duniya yana samun farfadowa sannu a hankali, amma ko da haka rashin tabbaci yana kansancewa. Kuma ana fuskantar kalubale yayin da ake kawar da rikicin hada-hadar kudi na duniya da kuma farfado da bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Sabo da haka, taken taron kolin a wannan karo shi ne "warware matsala domin samun bunkasuwa tare".

Batun darajar kudin musaya ya zama batun farko da ya fi jawo hankalin kasa da kasa. A rabin karshen shekarar bana, an tattauna batun yakin kudi a fadin duniya, kasashe masu yawa sun dauki matakan sa hannu kan darajar kudin musaya don magance canjin darajar kudin musaya dake kawo illa ga tattalin arzikinsu. A gun taron ministocin kudi na kungiyar G20 da shugabannin bankunan tsakiya na duniya da aka yi a birnin Gyeong Ju dake kasar Koriya ta kudu a karshen watan Oktoba, kasashe membobin kungiyar G20 sun yi alkawarin daukar matakan kudi don tabbatar da farashin kayayyaki da sa kaimi ga farfado da tattalin arziki. Amma kasar Amurka ta gabatar da manufar kudi mai sassauci a zagaye na biyu a wannan wata, wadda ta sa kasa da kasa suka nuna damuwa kanta. Mataimakin ministan kudi na kasar Sin Zhu Guangyao ya bayyana cewa, zai yi musayar ra'ayoyi tare da kasar Amurka game da wannan a gun taron koli na birnin Seoul.

Kafa tsarin tabbatar da tsaron hada-hadar kudi na duniya yana daya daga cikin manyan batutuwan da kasar Koriya ta kudu ta fi son tattaunawa a gun taron koli na birnin Seoul. Wannan batu ya zama babban batu da aka tattauna a gun taron ministocin kudi na kungiyar G20 da shugabannin bankunan tsakiya na duniya da aka yi a watan Afrilu na bana, bayan haka, ya fi jawo hankalin duniya sosai. Yanzu dai, kasashe membobin kungiyar G20 sun amince da wannan batu, watakila za su cimma daidaito kan yadda za a dauki matakai a taron koli na Seoul.

Bayan rikicin hada-hadar kudi na duniya a shekarar 2008, an samu ci gaba wajen yin kwaskwarima kan tsarin kudi na duniya, sabbin kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki a duniya da kasashe masu tasowa sun kara samun ikon yin magana da tsara manufofi. Kasa da kasa suna fatan za a sa kaimi ga yin kwaskwarima kan tsarin kudi na duniya a gun taron koli na Seoul, da kara baiwa sabbin kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki a duniya da kasashe masu tasowa ikon yin magana da wakilci a hukumomin kudi na duniya.

Batun samun bunkasuwa shi ne batu mafi tasiri a karo na farko da ya zama muhimmin batu da za a tattauna a taron koli na kungiyar G20. Shugaban kasar Koriya ta kudu Lee Myungbak ya yi fatan cewa kasa da kasa za su yi kokari tare don taimakawa kasashe masu tasowa wajen raya kasa, da kuma kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China