in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan atisayen sojan yaki da ta'addanci na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai
2010-09-15 21:22:03 cri
Masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. A cikin shirinmu na yau, kamar yadda muka saba, za mu fara da karanto wasu wasikun da muka samu daga wajenku. Da farko ga wannan sako daga malam Shuaibu Muhammed a jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya, inda ya rubuto mana cewa, "Wani abin bakin ciki yanzu haka ruwa ya mamaye kauyuka da dama a jihar kebbi, ambaliyar ruwa ta abkawa garin Argungu, da kauyuka da yawa, haka kuma ruwa ya yi sanadiyar hasarar amfanin gona, da dukiya ta miliyoyin Naira. Karamar Hukumar Bunza, da kauyukanta suna cikin wannan ambaliyar ruwa"

To, malam Shuaibu Muhammed,abin sai addu'a. A bana, an gamu da bala'u da dama a wurare daban daban. Kamar kasar Sin, an sheda ambaliyar ruwa mai tsanani a nan, yayin da Rasha ta gamu da matsalar wutar daji. Yanzu ambaliyar ruwa tana addabar jihar Kebbi. Duk da haka, mun yi imani cewa, dukkanmu za mu yi nasara a karshe ta hanyar nuna juriya da taimako daga kasa da kasa. Allah ya taimake mu, amin.

Sakon malam Shuaibu Muhammed ke nan. Bayan haka, malam Sanusi Isah a Nasarawa, tarayyar Nijeriya ya bayyana mana cewa, "A kullum ni kan nuna kaunata ga sashen hausa na rediyon kasar Sin dangane da kokarin da kuke yi na ilmantar da mu masu sauraro a kan halin da duniya take ciki. Sabo da haka kun cancanci yabo, tare da addu'a Allah ya karawa wannan tashar rediyo farin jini a ko ina cikin duniya. Bayan haka sashen hausa, ina son ku kara bunkasa shirye-shiryenku, har ma ya fi kowace tashar rediyo a duniya."

To, mun gode, malam Sanusi. Lallai kana mai da hankali kan shirye-shiryenmu a kullum. Kuma muna farin cikin samun amincewa daga wajenka. Ko shakka babu, za mu kara kokari a nan gaba. Da fatan za ka kara turo mana shawarwari masu kyau. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin.

Sakon malam Sanusi ke nan. To, masu sauraro, a kwanan baya, malam Lawal Abubakar daga Bauchi, tarayyar Nijeriya ya yi tambayar cewa, "Na ji an ce kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai za ta yi atisayen soja, ko ba haka ba?" E, haka ne, malam Lawal, yanzu za mu yi kokarin bayar da cikakken bayani kan lamarin, da fatan kana sauraronmu.

A kwanan baya, hakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya shelanta cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai za ta yi atisayen sojan kyamar ta'addanci cikin hadin gwiwa a kasar Kazakhstan daga ran 9 zuwa ran 25 ga watan Satumba, takensa shi ne "Peace Misson---2010".

Wani masani kan aikin soja manjo janar Yin Zhuo ya yi nuni da cewa, ba kamar yadda yake a da ba, a wannan karo, kasar Sin ta kara yin la'akari da bukatun yake-yake a yayin tura sojoji. Yin ya ce,

"Game da kasar Sin, alamar atisayen soja a wannan karo ita ce dacewa da bukatun hakikanin yaki sosai. Mun iya gano lamarin bisa sojojin da muka tura. Ba mu tura wasu sojojin dake da matsayin koli ba. Kuma makaman da wadannan sojoji suke amfani da su su ne makamai ne da sojojin kasar Sin suke amfani da su a halin yanzu."

An kafa kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a shekarar 2001, membobinta sun hada da Sin, Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan, da Uzbekistan. Fadin kasashe membobin kungiyar ya kai sama da murabba'in kilomita miliyan 30 baki daya, wanda ya kai kashi uku bisa biyar na fadin nahiyar Asiya da na Turai. Yawan mutane ya kai biliyan 1.5, wanda ya kai kashi daya bisa hudu na duniya baki daya. Babban mai ba da shawara na cibiyar kula da manyan tsare-tsaren duniya ta Sin, manjo janar Wang Haiyun dake kula da yanayin da ake ciki a wannan yanki ya kyautata zaton cewa, yankin tsakiyar Asiya da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai take kasancewa yana tsakiyar yankin Turai da Asiya, inda akwai matsaloli da rikice-rikice da dama. Wang ya bayyana cewa,

"A cikin 'yan shekarun da suka gabata, wadannan kasashe suna kyautata tsarin kasa, da canza hanyar bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma. A sabili da haka, suna gamuwa da wasu matsaloli a fannin kyautata harkokin zamantakewar al'umma. Bugu da kari, mafi yawansu suka kasancewa a baya wajen bunkasa tattalin arziki. Shi ya sa suna gamuwa da matsaloli da yawa. Bayan haka, mazaunan wurin suna bin addinai daban daban. Shi ya sa akwai matsaloli da dama a wannan fanni."

A cikin shekarun da suka wuce, 'yan ta'adda, 'yan a-ware, da masu tsattsauran ra'ayi suna kara aiwatar da danyun ayyuka a wannan wuri. Game da kasar Sin kuma, iyakar kasa ta yamma tana makwabtaka da kasa da kasa dake tsakiyar Asiya. A sakamakon haka, shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a wadannan kasashe na da alaka da kasar Sin sosai. Mataimakin shugaban kwalejin nazari kan dangantaka tsakanin kasa da kasa na jami'ar jama'ar kasar Sin Farfesa Jin Canrong ya bayyana cewa, ta yin la'akari da matsin lamba da wadannan bangarori uku suke yi, hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya baki daya zai zama kyakkyawar hanya wajen yaki da su. Jin ya ce,

"A hakika dai, wadannan kasashe suna a baya a fannin fasahohi da tattalin aziki. A sabili da haka, yayin da suke fuskantar wadannan bangarori uku, musamman ma ta'addanci, a ko da yaushe su kan gaza sosai wajen yaki da su. A daidai wannan lokaci, hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa zai ba da babban taimako a gare su duka."

Ban da yin atisayen soja, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai tana kara karfin kasashe membobinta na yaki da ta'addanci ta hanyoyi daban daban. Game da lamarin, manjo janar Wang Haiyun ya bayyana cewa,

"Alal misali, an kafa cibiyar shiyya-shiyya ta yaki da ta'addanci. Sau da dama an dora muhimmanci kan batun yaki da ta'addanci a yayin ganawar shugabannin kasa da kasa. Bayan haka, hukumomin yanke hukunci na kasashen membobin kungiyar suna kara hada gwiwa a wannan fanni a yau da kullum, ciki har da canza sakwannin sirri, tabbatar da kungiyar ta'addanci da dai sauransu. Hadin gwiwa tsakaninsu a fannin aikin soja kuma na samun karfafuwa ta hanyar yin atisayen soja da ganawar ministocin tsaron kasa da dai sauransu."(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China