in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Su Ping, sarauniyar wakokin Hua'er da ta hada gargajiya da kirkire-kirkire tare wajen wakokin
2010-09-15 20:38:01 cri
Wakoki masu salon Hua'er wakoki ne da ke samun karbuwa kwarai da gaske a lardunan Gansu da Qinghai da Ningxia kana da Xinjiang da dai sauran yankunan da ke arewa maso yammacin kasar Sin, wadanda suke da dogon tarihi. Yayin da ake gada da kuma raya wakokin Hua'er, an samu dimbin mawakan da suka nuna gwaninta sosai a wannan fanni, wadanda suka yada wakokin daga gonaki zuwa dandalin wakoki na duniya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da labarin Su Ping, wata musulma 'yar kabilar Sala da ake kiranta sarauniyar wakokin Hua'er.

Madam Su Ping mai shekaru 68 da haihuwa an haife ta ne a cikin wani gidan musulmai 'yan kabilar Sala da ke gundumar Hualong ta lardin Qinghai. A matsayinta ta daya daga cikin kabilu goma da ke bin addinin Musulunci a kasar Sin, 'yan kabilar Sala sun nuna sha'awa sosai ga wakokin Hua'er tun kaka da kakaninsu, ko manoma ko masu jan kwale-kwale dukkansu sun iya rera wasu wakokin Hua'er. Sakamakon kasancewar irin wannan yanayin al'adu, Su Ping ta nuna matukar sha'awa ga wakokin Hua'er tun yarantakarta, kuma bisa muryarta mai dadin ji, ta yi dan suna a dandalin rera wakokin Hua'er. Yayin da take tabo magana kan karon farkon da ta rera wakokin Hua'er a dandali, Madam Su Ping ta bayyana cewa,

"yayin da shekaruna suka kai 9 da haihuwa, na fara rera wakokin Hua'er a bikin nune-nune. A wancan lokaci, kasar Sin ta samu 'yancin kai ba da jimawa ba, domin murnar aikin yin kwaskwarima ga tsarin mallakar gonaki, kungiyar aiki ta kauyenmu ta gabatar da ni wajen rera wakoki. Sabo da ba ni da tsayi a wancan lokaci, sai na tsaya a kan tebur na rera kamar haka:' manyan tsaunuka sun canja zuwa rumfunan adanar hatsi, madatsan da ba a iya samun ruwa ko kadan a ciki kuma sun canja zuwa gonaki. 'Yan mata sun sanya sabbin tufafi masu kayatarwa, wadanda su yi kama da furanni masu kyan gani.'"

Su Ping ba ta gamsu da wannan karamar nasara da ta samu ba, a maimakon haka, ta kara sha'awarta ta fuskar rera wakokin Hua'er. Sakamakon kokari da kuzarin da ta yi, ba kawai Su Ping ta samu karbuwa daga mutanen garinta ba, hatta ma ta samu amincewa daga kwararru a fannin wakokin Hua'er. Yayin da shekarunta suka kai 17 da haihuwa, Su Ping ta shiga cikin kungiyar wake-wake da raye-raye ta lardin Gansu, da kuma fara zaman rayuwarta a matsayin wata mawakiya. A shekara ta 1982, yankin Linxia ta lardin ya shirya bikin murnar sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin, inda ya kuma gayyace ta wajen rera wakokin Hua'er tare da mawaka na sauran wurare. wakar da Su Ping ta nuna ta samu karbuwa sosai daga jama'a 'yan kabilu daban daban, abun da kuma ya ba da tunanin shirya taron kide-kide da wake-wake na Hua'er. Kamar yadda Madam Su Ping ta fada:

"A lokacin da, mutane su kan boye kansu a cikin bishiyoyi don saurarar wakokin Hua'er. Amma bayan da suka ji wakar da na rera a gun bikin murnar sabuwar shekara, mutane sun fara nuna kauna sosai ga wakokin. Don haka ni da wasu mawaka mun shirya babban dandalin kide-kide da wake-wake na Hua'er, wanda ya sha bamban sosai tare da wanda a kan yi a zaman yau da kullum, wato mata da maza su kan rera wakokin Hua'er a tsakaninsu don neman soyayya. Ni mutumiya ce ta farko wajen shirya babban dandalin kide-kide da wake-wake na Hua'er."

Daga baya kuma, bisa kaunar da ta nuna wa wakokin Hua'er, Madam Su Ping ta shirya bukukuwan nuna wakokin Hua'er daruruwa a gundumomi fiye da 40 kana da wasu masana'antu da wuraran hakar ma'adinai da ke lardunan Gansu da Qinghai da Ningxia, wanda ya sa Su Ping samu lambar yabo ta "sarauniyar wakokin Hua'er".

A waje daya kuma, Madam Su Ping ta yi kirkire-kirkire kan hanyar rera wakokin Hua'er bisa tushen tsayawa kan bin hanyar gargajiya, wato ta yi amfani da fasahar bel canto wato amfani da lafazin murya wajen rera wakokin Hua'er, ta hakan ne ta daga wakokin Hua'er zuwa wani sabon mataki. Babban malami a fannin ilmin wakokin Hua'er Guo Zhengqing ya bayyana cewa, ta fuskar rera wakokin Hua'er, babu shakka Madam Su Ping kwararriya ce, ta ba da kyakkyawan misali wajen hada hanyoyin gargajiya da zamani tare wajen rera wakokin. Kuma ya kara da cewa,

"Ko a fannin harshe, ko a fannin yadda aka yi tunani, ko kuma a fannin bayyana abubuwan da ake ji a rai, Madam Su Ping ta yi iyakacin kokari wajen bin takin zamani da kuma nuna yanayinta na musamman, amma ta yi haka ne bisa tushen kiyaye abubuwan gargajiya. Don haka wakokin da Su Ping ta rera ta samu karbuwa kwarai da gaske daga jama'a."

A ganin Su Ping, idan ana son burge masu sauraro, to dole ne a samu kwarewa sosai. A wajen mawaki ko mawakiya, samun amincewa daga jama'a abu ne mafi muhimmanci. Sabo da kaunar da aka nuna mata, Madam Su Ping tana ta samun kwarin gwiwa a kan hanyar rera wakokin Hua'er. A shekara ta 1984, Su Ping ta rera wakokin Hua'er uku a gun bikin murnar sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin da gidan talibijin na CCTV ya shirya, wanda ya sa wakokin Hua'er suka samu karbuwa a duk fadin kasar Sin.

Sakamakon wannan wakar Hua'er mai dadin ji, Madam Su Ping ta samu damar shiga dandalin wakoki na duniya. Daga shekaru 80 na karnin da ya gabata, ta yi ta rera wakokin Hua'er a yankunan HongKong da Macao da Taiwan na Sin kana da kasashen Koriya ta Arewa da Austria da Jamus da Faransa da Italiya bisa gayyatar da aka yi mata. Sakamakon kokarin da ta yi wajen yada wakokin Hua'er a Asiya da Turai da Afirka, mutanen ketare suna nuna jin dadin wakokin gargajiya na kasar Sin, hakan ya kara sunan wakokin Hua'er. Margret Liate daga kasar Amurka ta bayyana cewa,

"Ban taba jin wakokin Hua'er ba a lokacin da, balle ma na san cewa, wannan wata wakar gargajiya ce ta kasar Sin. Bayan da na ji wakokin Hua'er da Madam Su Ping ta rera, na fara fahimtar wakokin. Ina son waka mai taken 'kyakkyawan Fure na saurayi' da ta rera, wadda take da dadin ji kwarai. Sakamakon wakar kuma, na nuna kauna sosai ga wakokin Hua'er nan da nan."

Ba kawai Madam Su Ping ta samu manyan nasarori wajen rera wakoki ba yanzu, har ma ta samu kyawawan sakamako wajen nazarin salon wakokin Hua'er. Tana ta tattara kide-kiden Hua'er daga wajen jama'a, da nazari kan tarihi da sassan Hua'er, kana da buga littattafai da yawa a wannan fanni. Ban da wannan kuma ta kan shiga makarantu don yada ilmin wakokin Hua'er, a kokarin bayar da babbar gudummawa wajen bunkasuwar wakokin Hua'er.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China