in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar UNESCO tana bikin yada al'adun Confucius na tsawon mako guda
2010-09-07 16:17:52 cri
Confucius shi ne wani babban mai tunani, mai falsafa kuma mai ba da ilimi. Ba kawai Confucius ya taka muhimmiyar rawa ga tarihi da al'adun kasar Sin cikin tsawon lokaci ba, har ma ya ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar zaman al'ummar dan Adam. Daga ran 6 zuwa ran 10 ga wata, a ma'aikatar al'adun kasar Sin, da ma'aikatar ba da ilimi, da kwamitin hukumar UNESCO, da kuma gwamnatin lardin Shandong ta kasar Sin sun yi bikin yada al'adun Confucius na tsawon mako guda a birnin Paris, hedkwatar hukumar UNESCO.

Wannan bikin da ake yi a hedkwatar hukumar UNESCO shi ne bikin yada al'adu mafi girma kuma mafi tattara yawan mutane da gwamnatin kasar Sin ta yi a hukumar a shekarun baya. Don gudanar da bikin da kyau, kasar Sin ta aika tawagar hada mutane sama da 80 zuwa Paris don halartar bikin. Bisa matsayin mai jagorancin tawagar, madam Zhao Shaohua, mataimakiyar ministan al'adun kasar Sin ta mai da wannan biki tamkar wata irin mu'amala a tsakanin kasa da kasa. Ga abin da ta ce,

"Ba kawai an gada tare da rike ra'ayoyin Confucius a kasar Sin cikin tsawon shekaru dubai ba, hatta ma, mutanen da yawa na kasa da kasa suna mai da hankali kan wadannan ra'ayoyi sosai. Sabo da haka, mun gadi ra'ayoyin Confucius kuma muna yada su a duniya."

A gun bikin, za a nuna hotuna da yawa, kuma za a nuna kayayyakin musamman na kasar Sin ga abokanmu na Faransa. Ban da haka kuma, bangaren shirya bikin ya dauki niyyar yada ra'ayoyin Confucius ta hanyar yin kide-kide da raye-raye.

A wannan rana, Jean-Pierre Raffarin, tsohon abokin jama'ar kasar Sin kuma tsohon firaministan kasar Faransa ya halarci bikin. Bayan da ya kalli bikin, ya ce,"Gwamnatin kasar Sin da hukumar UNESCO sun shirya wannan biki tare, wannan na da muhimmiyar ma'ana. Da farko, ta wannan biki, muna iya gadon ra'ayoyin Conficius wadanda suke kawo moriya ga jama'ar kasar Sin, kuma suka kawo moriya ga jama'ar duniya. Wadannan ra'ayoyi su ne ra'ayoyi na lokacin da, amma hukumar UNESCO ta ba su ma'ana ta lokacin zamani."

Davidson L. Hepburn, shugaban babban taron hukumar UNESCO ya ziyarci bikin nune-nunen hotuna dake bayyana Confucius. Yana ganin cewa, wannan biki ya samar da wata dama ga mutane mafi yawa wajen fahimtar Confucius. Ya furta cewa, "Ya kamata mu kara sanin Conficius da ra'ayoyinsa. Sai wannan biki zai samar da dama ga mutane domin kara fahimtar wannan babban mutumi da ra'ayoyinsa. Ina farin ciki sosai domin ziyara wannan biki."

Wata 'yar kallo mai suna Caroline ta kwashe tsawon lokaci tana duba gabatarwar Conficius, ta ce, "Ina ganin cewa, ra'ayoyin Conficius suna mai da hankali kan girmama mutane da samun jituwa. Na taba zuwa kasar Sin na ziyarci kabarin Conficius dake birnin Qufu. Ziyara a wancan lokaci ta burge ni sosai."

Abin musamman na wannan biki shi ne a ran 8 ga wata, hukumar UNESCO za ta yi bikin ba da lambar kyauta ta wayar kan jama'a game da ra'ayoyin Conficius. Wannan ne wata muhimmiyar lambar kyauta da gwamnatin kasar Sin ta kafa a fannin ba da ilimi.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China