in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarwarin tattalin arzikin tsakanin Sin da Japan na amfanawa kasashen biyu
2010-08-30 18:39:58 cri

A ran 28 ga wata da dare, an rufe taron shawarwarin tattalin arzikin tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Japan a karo na uku a nan birnin Beijing. Mr. Wang Qishan mataimakin firaministan kasar Sin da Mr. Katsuya Okada ministan harkokin waje na kasar Japan suka jagoranci wannan shawarwari, bangarorin biyu sun yi tattaunawa sosai kan batuttuwan da suka shafe hadin gwiwar tattalin arzikin da ke tsakaninsu. A ran 29 ga wata, Mr. Zhang Jifeng direkatan ofishin nazarin tattalin arzikin kasar Japan na cibiyar kimiyyar zaman rayuwa na kasar Sin ya gana da wakilinmu, inda ya nuna cewa, wannan shawarwari za su samar da kyakkyawan sakamako kuma yana da muhimmiyar ma'ana ga tattalin arzikin kasashen biyu.

A watan Afrilu na shekarar 2007, firaminista Wen Jiabao na kasar Sin da tsohon firaminista Sinzo Abe na kasar Japan sun kafa tsarin yin shawarwarin tattalin arzikin tsakanin manyan jami'an kasashen biyu. An taba yin wannan tattaunawa a watan Disamba na shekarar 2007 da watan Yuni na shekarar 2009, Shawarwari da suka zama wani muhimmin batun da ke karfafa huldar moriyar juna.

Game da kyakkyawan sakamakon da aka samu a shawarwari na wannan karo, Mr. Zhang Jifeng ya nuna cewa, "Huldar tattalin arzikin da ke tsakanin kasashen Sin da Japan tana bunkasuwa lami lafiya, kara yin shawarwarin tsakanin mayan jami'an bangarorin biyu na da muhimmanci. Game da shawarwari na wannan karo, da farko, sun yi musanyar ra'ayoyi kan wasu muhimman batuttuwa kuma sun sami ra'ayi daya. Na biyu, sun daddale yarjejeniyoyin yin hadin gwiwa guda 7 wadanda ke da nasaba da muhalli, masana'antu, hada-hadar kudi, da kiyaye daji."

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China