in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayani kan 'yar wasan sinima Audrey Hepburn
2010-08-17 15:50:32 cri

Jama'a masu karanta, muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Kuma muna yi muku godiya sosai sabo da kokarinku na aiko da wasiku, da fatan za ku ci gaba da yin musayar ra'ayi tare da mu ta hanyoyin bugo wayar tarho, aiko da sakwanni ko E-mail da dai sauransu. Sai mun ji daga wajenku.

To, a cikin shirinmu na yau, da farko za mu karanto wasu wasikun da muka samu daga wajenku. Ga wannan sako daga malam Bashir Maishanu Yauri a jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya, inda ya bayyana cewa, "Gaskiya a tarihin bikin Expo da aka gudanar har sau 41, babu wata kasa da ta biya bukatun masu halartar wannan bikin sai kasar Sin, idan muka yi la'akari da yadda kasar Sin ta samar da wadataccen wurin, inda kasashe masu halartar suka kafa rumfunansu, tare da samarwa jama'a cikakken tsaro. Haka zalika a wajen 'yan jarida sun more sosai, sabo da yadda kasar Sin ta samar musu ingantaccen wurin watsa labaransu kai tsaye, tare da ba su damar daukar hotunan bidiyo. Ban da wannan kasar Sin ta yi shiri na ganin yadda za a samu tsarin birane a nan gaba a kowace kasa ta duniya. Daga karshe, ina mika godiya bisa yadda gwannatin kasar sin take taimakawa kasashen nahiyar Afrika, ta fannin taimakawa wurin kafa masana'antu fadada hanyar sadarwa. Ina kuma mika godiyata musamman ga ma'aikatan Sashen Hausa na Chana radio International, Allah ya bar zumunci, ya kuma ba ku karfin gwiwar ba mu labarai a kowane lokaci ."

To, mun gode, malam Bashir. Yanzu ana gudanar da bikin baje kolin duniya a Shanghai yadda ya kamata. Kuma masu yawon shakatawa na kasa da kasa su kan kawo ziyara a kowace rana. Muna fatan masu sauraronmu za ku samu damar kawo ziyara a birnin Shanghai. Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu, amin!

Sakon malam Bashir ke nan. Bayan haka, malam Ali Buge Kiragi daga jihar Yobe, tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, "Na samu sakonku na fatan alheri tare da sanar da ni cewa, kun samu sakon da na aiko muku. Hakika mutune har ce mun suke yaushe ne za ka samu kyautar masamman, wato ta kawo ziyara zuwa kasar Sin ta zamani? Inda nake ce musu, ai komai na Allah ne, idan da rabona zai kai ni yin ziyara a kasar Sin. Duk da cewa ban taba yin nasara ba, zan ci gaba da hulda da ku da kuma shiga gasar kacici-kacici da kuke shiryawa lokaci zuwa lokaci. Na gode. Allah ya bar zumunci tsakaninmu har abada, amin."

To, mun gode, malam Ali. Sakonka ya burge mu sosai. Mun yi farin ciki da halartarka a gasar kacici-kacici da muke shiryawa. Da fatan za ka yi nasara a wannan karo. Allah ya taimake mu, amin.

Sakon malam Ali ke nan. A kwanan baya, malam Musa Abbas a Bauchi, tarayyar Nijeriya ya yi mana tambayar cewa, "Don Allah ko za ku iya ba ni wani bayani dangane da tarihin madam Audrey Hepburn?" To, yanzu za mu kokarta amsa wannan tambaya.

Audrey Hepburn, shahararriyar 'yar wasan sinima, wadda ta taba samun kyautar Oscar. Bayan da ta tsufa, ta zama wakiliyar musamman ta asusun yara na MDD. A shekarar 1999, cibiyar fina-finai ta Amurka ta zabe ta a matsayi na uku na wata 'yar wasan sinima da aka fi nuna mata girmamawa a shekaru 100 da suka gabata.

An haifi Audrey Hepburn a birnin Brussels na kasar Belgium a ran 4 ga watan Mayu na shekarar 1929. Yayin da shekarunta suka kai 6 da haihuwa, Hepburn ta shiga wata makarantar 'yan gata dake birnin London na Birtaniya domin yin karatu. Amma a daidai wannan lokaci, mahaifinta yana nuna goyon baya ga Nazi. A sabili da haka, a wata rana ba zato ba tsammani ya bace, ba tare da yin ban kwana da iyalansa ba. Lamarin ya girgiza hankalin Hepburn sosai. A shekarar 1938, mahaifanta suka kishe aurensu a hukunce. Bayan shekara daya kawai, Hepburn ta kai ziyara a gidan kakarta a Holland tare da mahaifiyarta, inda ta shiga kwalejin kide-kide mai suna Arnhem a kokarin koyon raye-rayen Ballet. Daga bisani, yakin duniya a karo na biyu ya barke, sojojin Nazi suka mamaye Holland. A sakamakon asalin iyalan mahaifiyarta na Yuhudawa, Hepburn ta gamu da matsaloli da dama tare da shan wahalhalu. Duk da haka, Hepburn ta yi iyakacin kokari domin ba da taimako a yaki da bangaren Fascist.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China